24/03/2026
MAULANA SHEIKH ADAM BADAMAGARE. (SHAIBATUL HAMDI) AZARE
#قد مات قوم وما ماتت فضائلهم
وعاش قوم وهم في الناس أموات
Masu Hikima Suna cewa;
Hakika Wasu Mutane( Mutanen Kirki) sun mutu Amma Falalarsu da Alkhairinsu Bai Kare ba sai aga tamkar Suna Raye.
Sannan Kuma wasu Mutane(Mutanen Banza) Suna Raye Amma matattu ne Saboda ba Alkhairi a tare dasu.
Cikin Yardar Allah da Falalarsa A Ranar 22nd March, 2026. Qunqiyar Matasa Yan Qasar Katagum s**ayi taro na Musamman don murnar cikar Qasar Katagum Shekara 50 da zama Local Government, a inda ta Zabi wasu daga cikin fitattun mutane da s**a taka rawar Gani wajen cigaban Qasar Katagum. Alhamdulillahi cikin Wadanda aka zaba don Karramasu akwai MAULANA SHEIKH ADAM BADAMAGARE (SHAIBATUL HAMDI) Hakika wannan Lamarin bai zo mana da mamaki ba duba da yadda MAULANA SHEIKH ADAM BADAMAGARE ya zama shine Daya tilo da ya Taimaka Matuqa wajen Assasa Harkar Ilimi da yadda ya Ilimantar da mutane bila Adadin ba ma a Qasar Katagum ba Har a Arewacin Nigeria Gaba Daya. Don Kusan bincike ya Tabbatar Cewa SHEIKH ADAM BADAMAGARE shi ya fara Assasa makarantar ISLAMIYYA a Qasar Katagum Ko ince a Arewacin Nigeria Gaba Daya.
Bayan nan SHEIKH ADAM BADAMAGARE shine a Kaf Kasar Katagum yake da Gidan Baqi wadda ya ginashi ne Musamman saboda saukar Baqi idan s**azo, wannan Kuwa ya dace da Hadisin Sayyiduna Rasulullahi da yake cewa من كان يؤمن بالله واليوم الآخر فليكرم ضيفه.
Wato duk wadda yayi Imani da Allah da ranar Qarshe to ya Girmama Baqonsa. Sannan anyi wani Zamani a baya da akayi fama da tsananin fari da Rashin Abinci a Qasar Katagum, Alhamdulillahi SHEIKH ADAM BADAMAGARE shine cikin ilimin da Allah ya bashi ya fitar da wasu Auradai na neman Sauki da Rahamar Allah kan samun Abinci isashshe, wadannan Auradai sune Lahaula walakuwwata, da Hasbunallahu, da Kuma ya Ladifu don Allah ya Kawo mana saukin wannan fari da yunwa wadda tunda ya fitar da wadannan Auradai ake Karantasu Har yau a Azare dai kan ba'a taba Samun irin wannan musiba ba. Kuma Alhamdulillahi Haryanzu ana Karanta wadannan Auradai a Zawiyyarsa da ta Almajiransa. Alhamdulillahi Gudumawar da SHEHI ya bayar a Qasar Katagum da Arewacin Nigeria bazasu Qirgu ba.
Allah ya Sakawa MAULANA SHEIKH ADAM BADAMAGARE Da Mafificin Alkhairi. Ya Bamu Albarkacinsa. Muna Addu'a da Fatan Alkhairi ga wannan Qungiya ta Matasa,
KATAGUM YOUNGER GENERATION FORUM