Sheikh Idris Badamasi Idris

Sheikh Idris Badamasi Idris

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sheikh Idris Badamasi Idris, Tutor/Teacher, Aminu Kano Crescent, Wuse II, Abuja.

23/05/2025

Idan har kana son zama hamshaƙin mai kuɗi; to ka daina tunani irin na 'yan albashi.

22/05/2025

Idan ya zamana ba ka gani sai abin da kaɗai haske ya haska, hakanan ba ka ji sai abin da kaɗai baki ya furta; to a haƙiƙa ba ka ji kuma ba ka gani.

22/05/2025

Arziƙi da kuɗi suna farawa ne daga tunani, sai su tabbata ta hanyar imani da kuma aiki mai ɗorewa.

21/05/2025

Yaro yana faɗuwa sama da sau 50 kafin ya koyi tafiya, amma bai taɓa tunanin ya daina gwadawa ba.

04/05/2025

Fassarar Littafin:

"MEN ARE FROM MARS, WOMEN ARE FROM VENUS, na John Gray. A taƙaice.

Daga Idris Badamasi Idris ✍🏼

Rubutu na biyu.

MANUFAR LITTAFIN:

Don taimakawa ma'aurata ko masoya su fahimci juna sosai.

Don rage saɓani da fahimtar juna bisa banbancin ɗabi'ar da Maza da Mata ba su fahimci juna a kai ba.

Don inganta soyayya, zaman lafiya, da yarda tsakanin Maza da Mata.

SAƘO NA MUSAMMAN DAGA LITTAFIN:

Domin zama lafiya da fahimtar juna tsakanin Maza da Mata; Ba sai an canza mace ta zama namiji ba, ko kuma an canza namiji ya zama mace ba, A'a. Sai dai kawai kowa ya fahimci ɗan uwansa a haka, a yadda yake, sai ya mu'amalance shi cikin hikima da sanin ya kamata, Shikenan.

GABATARWA:

A cikin wannan littafi, marubucin "John Gray" ya bayyana wata muhimmiyar fahimta ce cewa: Maza da Mata suna da banbanci sosai, kamar dai ka ce sun fito ne daga wasu duniyoyi biyu mabanbanta, Maza daga Mars, Mata kuma daga Venus.

Saɓani tsakanin Namiji da Mace ba yana nufin cewa ɗaya yana kan kuskure bane ɗaya kuma yana kan daidai ba, A'a. Yana nuna cewa kowannensu yana da halayensa ne, buƙatunsa, ɗabi'unsa, yadda yake kallon al'amura, da hanyar tunaninsa ne ta daban.

Wannan banbanci da ke tsakanin Maza da Mata shi ne tushen rashin fahimtar juna a tsakanin Ma'aurata. Amma da zarar kowa ya fahimci inda ɗan uwansa ya fito da kuma inda ya dosa, da halayensa, da ɗabi'unsa; to sai a zauna lafiya.

Littafin yana koya mana yadda za mu fahimci juna, girmama juna, da mu'amala da juna cikin hikima, maimakon mu yi ta saɓani da ganin laifin juna.

Za mu Ci gaba In sha Allah.

03/05/2025

Fassarar Littafin:

"MEN ARE FROM MARS, WOMEN ARE FROM VENUS, na John Gray." A taƙaice.

Daga Idris Badamasi Idris ✍🏼

Rubutu na farko.

MA'ANAR LITTAFIN:

Babbar ma'anar littafin ita ce ce wa: Maza da Mata su na da halaye ne daban-daban, kai ka ce dai kamar sun fito ne daga wasu duniyoyi biyu mabanbanta, kuma haka ne.

BABBAN ABIN DA LITTAFIN KE KOYARWA:

Littafin ya na koyar da yadda Maza da Mata su ke da halaye daban-daban: wajen tunani, magana, nuna soyayya, da kuma mu'amala.

Marubucin ya yi amfani ne da ƙirƙirarren misali na nuna ce wa Maza sun fito ne daga wata duniya ta daban mai suna Mars, Mata kuma daga Venus. Domin ya bayyana banbancin ɗabi'unsu da yadda suke kallon al'amura.

MUHIMMAN BATUTUWAN DA LITTAFIN YA ƘUNSA:

1. Halayen Maza:

Maza yawanci suna so ne su warware matsala, da kansu.

Ba sa son surutu ko magana da yawa idan suna cikin damuwa, suna janyewa ne su keɓe kamar suna cikin "kogo".

Suna son a girmama su, a yarda da su.

2. Halayen Mata:

Mata suna son surutu, suna jin daɗin magana, da bayyana abin da ke ransu.

Suna son kulawa, da jin ce wa ana sauraren su.

Suna son kawai haɗin kai ne daga Maza, kuma a fahimce su haka, ba wai a gyara su ko a magance matsalar ba.

3. Matsalolin Zamantakewar Aure:

Sau da yawa, matsala tsakanin ma'aurata na faruwa ne saboda kowane bangare yana kallon abubuwa ta hanya daban.

Maza suna ƙoƙarin gyara matsala, mata kuma suna so ne kawai a fahimce su kawai.

Yadda maza ke nuna soyayya ya sha banban da yadda mata ke so a nuna musu soyayya.

Za mu Ci gaba In sha Allah.

Want your school to be the top-listed School/college in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Address

Aminu Kano Crescent, Wuse II
Abuja