Atiku Online Community

Atiku Online Community This is a personal page that will promote, and campaign for H.E Atiku Abubakar, for President 2027, under the platform of ADC.

Atiku Abubakar: Ciki Da Gaskiya, Wuƙa Ba Ta Huda Shi! Daga: Sirajo Maikuɗi Mohammed"A shekarar 1993, lokacin da na fara ...
14/09/2026

Atiku Abubakar: Ciki Da Gaskiya, Wuƙa Ba Ta Huda Shi!

Daga: Sirajo Maikuɗi Mohammed

"A shekarar 1993, lokacin da na fara shiga takarar Shugaban Ƙasa, na shirya da tsara abubuwan da nake son yi wa Nijeriya. Na yi imani cewa ƙasar tana buƙatar sabon salon shugabanci wanda zai dogara da ƙwarewa da aiki da gaskiya, ba wai kawai ci gaba da tsofaffin hanyoyin gudanar da gwamnati ba.

Na yi imani da cewa, dole ne a sake duba tsarin gudanar da gwamnati domin a samu hanyoyin magance matsalolin da suke fuskantar jama’a.

Wannan fahimta ta samo asali ne daga yadda na gudanar da rayuwata. Na san ma’anar talauci, na san zafin rashin wadata, kuma na san irin wahalar da iyali ke fuskanta idan babu abin dogaro.

Na yi wa gwamnati aiki kusan shekara ashirin kafin na koma harkar kasuwanci da siyasa. Bayan haka kuma na shafe fiye da shekara talatin da biyar ina cikin harkokin siyasa, ciki har da shekara takwas da na yi a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Haka kuma, na fahimci cewa shugabanci ba mallakar mutum guda ba ne, shugabanci amanar jama’a ne."

Akwai wani abu da idan mu ka kalle shi sai mu ji dole ma mu marawa Alhaji Atiku baya. Kada mu manta gwamnatin nan ta APC...
08/09/2026

Akwai wani abu da idan mu ka kalle shi sai mu ji dole ma mu marawa Alhaji Atiku baya. Kada mu manta gwamnatin nan ta APC bayan ta cire tallafin fetur, wanda ko mahaukaci ya san daga nan ne matsalar ta soma, mun shiga wani yanayi na ƙuncin rayuwa da ba mu taɓa shigar irin sa ba.

Kuɗin da aka samu na rarar cire tallafin fetur ɗin babu wani ɗan ƙasa da zai iya faɗi maka cewa ga alfanunsa, amma haka gwamnatin ta ciwo bashin da babu wata gwamnati da ta taɓa ciwo irin sa, ƙasa da shekaru 4 an ciwo bashin tiriliyan 157. Ina kuɗin da aka cire tallafi, me ake yi da su? Kuɗin da ake ciwo bashi su ma suna ina?

Dukda haka kuma gwamnati da fito fili za ta ƙarɓi haraji daga yan ƙasa, yan kasuwa wanda dukkan mu mun san zalunci ne ƙarara. Sabidda siyasa sun kasa aiwatar da shirin, bayan sun ci zaɓe shi ne kuma aikin da za su fara yi. InshaAllah ta Allah ba ta su ba. Za mu kawar da gwamnatin su, za mu tabbatar da Alhaji Atiku.

Me Atiku Abubakar yake buƙata daga gareka?APC ta saki campaign organizations ɗin ta, wanda shine yake ƙara bamu tabbacin...
07/09/2026

Me Atiku Abubakar yake buƙata daga gareka?

APC ta saki campaign organizations ɗin ta, wanda shine yake ƙara bamu tabbacin zaɓen nan na gaske ne. Kuma ya riga ya taho. Duk wani shiri yanzu ne yake da amfani, haka kuma duk wata manufa ta ɗan takara, yanzu ne ya kamata ta yi aiki.

Akwai miliyoyin al'umma lungu da saƙo, birni da karkara. Suna buƙatar koda yaushe a ƙara nuna musu mahimmancin wannan tafiya da muke ciki yanzu haka.

Zaɓen 2027, zaɓe ne da zan iya cewa zai zo ta fuskoki da dama, wasu zasui amfani da ɓangaranci, addini ko yare. Saboda cimma manufar su.

Mu ƴan AA (Atiku/Amaechi) zamui amfani ne da ƙarfin gwuiwa, ƙuri'u, dogaro da Allah da kuma jajircewa wajen tabbatar da nasarar mu.

Zaɓe ne da zamui domin gyara goben mu. Zaɓe ne da dawo da tallafin man fetur, tattalin arziƙi, masana'antu, lafiya, wuta, noma da sauransu.

Babu abinda Atiku ko ADC take buƙata daga gareka daya wuce ƙuri'ar ka. Yarda da wannan tafiya da yaƙini cewar CANJI zai zo, da ƙarfin Ikon Allah da Taimakon sa.

Duk yadda zamui da ƙuri'un mu, mu tabbata mun kada APC da Tinubu. Mu tabbata dangin mu, Iyayenmu, ƙannen mu, da mutanen mu Atiku s**a zaɓa.

Atiku kuma yana buƙatar addu'a daga gareka saboda zaɓe da gwamnati, sai an dage da addu'a, neman taimakon Ubangiji da yaƙini cewar mune da nasara.

Ka gayawa wanda zaka gayawa, shima ya gayawa wanda zai gayawa, a sanar da wanda za'a sanarwa, a nusar da wanda za'a nusar, a kuma ankarar da wanda za'a ankarar cewar KAR A ZAƁI TINUBU.

A ZAƁI ATIKU domin ya dawo da tallafin MAN FETUR. Ya fuskanci TSARON ƘASA da gaske. A bawa MATASA AYYUKAN YI. A ƙirƙiri MASANA'ANTU, a tallafawa MANOMA, a kawo sauyi a ɓangaren WUTA, LAFIYA da ILIMI (Mafi mahimmanci koda yaushe). A ɗaukaka KASUWANCI, MANYAN AYYUKAN CI-GABA da kuma SAMAR DA SASSAUƘAR RAYUWA wa al'ummar Nijeriya.

Mu tabbata al'umma sun sani cewar idan TINUBU ya koma kan mulki, FAN FETUR zai ƙara tsada, rayuwa zata ƙara zafi da tsanani wa talakawan ƙasar nan.

Ku kula. Kuma ku lura.

03/09/2026
03/09/2026

Cire tallafin fetur: ko za ka iya faɗi mana wani alfanu da ka samu ta dalilin cire tallafin mai?

03/09/2026

Zancen Atiku kawai ake!

03/09/2026

Atiku Facebookers!

03/09/2026

Mu zabi Atiku, domin samun saukin rayuwa! 🤝

Address

Gwarinfa FCT Abuja
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Atiku Online Community posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category