NovaChain Academy

NovaChain Academy Africa's Hub for Blockchain & Web3 Education, Training the next generation of Blockchain & Web3 innovators.

WATA BIYU KACAL DA FARA TAFIYA! SHIN KUN SAN ABIN DA NOVACHAIN ACADEMY TA CIMMA?Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulil...
22/09/2026

WATA BIYU KACAL DA FARA TAFIYA! SHIN KUN SAN ABIN DA NOVACHAIN ACADEMY TA CIMMA?

Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!

Babu abin da zamu iya cewa ga Allah (SWT) bayan godiya a kan wannan babbar ni'ima da Ya yi mana ta samun gagarumar nasara cikin watanni biyu kacal da fara tafiyar NovaChain Academy, A cikin wannan ɗan ƙaramin lokaci, mun samu damar aiwatar da abubuwa da dama waɗanda s**a ƙara tabbatar mana da cewa tafiyar da muka fara tana da muhimmanci kuma tana da tasiri a cikin al'umma.

GAYYATAR MASANA DA MASU KWAREWA

Daga cikin abubuwan da muka gabatar a cikin waɗannan watanni biyu, mun gayyaci masana da ƙwararru daban-daban domin su zo su raba iliminsu da ƙwarewarsu tare da community ɗinmu, musamman a fannonin Web3, Blockchain da sauran fasahohin zamani.

Daga cikin waɗanda muka gayyata akwai:

- Mahmud Galadanci
- Sanusi Danjuma Ali
- Aliyu Samba
- Barr. Abdullahi-Hadee Isah Ibrahim
- Aliyu Dahiru Aliyu
- Ahmad XM, wanda wani uzuri ya hana shi samun damar halartar shirin.

Muna matuƙar godiya ga dukkan waɗannan ƙwararru bisa lokacin da s**a ba mu da kuma ilimin da s**a zo s**a raba tare da al'ummar NovaChain Academy. Hakika, al'umma ta amfana da gwala-gwalan ilimi daga gare su.

GOYON BAYAN AL'UMMAR CRYPTO

Haka kuma, mun samu gagarumin goyon baya daga ƴan Crypto, manya da ƙanana, waɗanda duk da cewa ba sa cikin shirin karatunmu kai tsaye, sun taimaka mana ta fannoni daban-daban bayan sun fahimci manufar da muke da ita da kuma irin sauyin da muke son samarwa a Arewacin Najeriya.

Daga cikin waɗanda s**a ba mu goyon baya akwai:

Chizo1germany, Rabi'u Biyo, Engr. Bakaka, Imamu Sheka da sauran waɗanda s**a taimaka mana ta hanyoyi daban-daban, Muna matuƙar godiya gare su, kuma muna addu'ar Allah Ya saka musu da alheri.

ƘARUWAR YARDA DA TASIRIN NOVACHAIN A CIKIN AL'UMMA

Alhamdulillah, muna ganin yadda mutane suke ƙara fahimtar manufar NovaChain Academy da kuma muhimmancin ilimin da muka zo da shi, Ɗaya daga cikin abubuwan da s**a ƙara tabbatar mana da hakan shi ne yadda muka samu ɗimbin mutane s**a yi registration domin fara karatunmu a ranar 1 ga Oktoba, 2026, duk da cewa tafiyar Academy ɗinmu ba ta wuce watanni biyu ba, wanda har yanzu ana ci gaba da samun sababbin masu registration.

Haka kuma, yadda social media platforms ɗinmu s**a samu ɗimbin mabiya cikin wannan ɗan ƙaramin lokaci ya ƙara tabbatar mana da cewa saƙonmu yana isa ga al'umma, kuma akwai mutane masu sha'awar samun ingantaccen ilimi a fannonin da muka mayar da hankali a kansu.

COMMUNITY ƊINMU A SOCIAL MEDIA

1. Facebook: muna da Mabiya 10,990 Link: https://www.facebook.com/share/1EQhfQ9FLg/

2. Telegram Channel: Muna da Mabiya 4,292 Link: https://t.me/NovaChainBA

3. WhatsApp Channel: Muna da Mabiya 2,478 Link: https://whatsapp.com/channel/0029Vb8pJ7l1t90lPzomgX0j

4. X (Twitter): Muna da Mabiya 1,364 Link: https://x.com/NovaAcademy01

MENENE MAKOMAR NOVACHAIN A SHEKARU BIYU MASU ZUWA?

Idan Allah Ya nuna mana wannan irin nasara cikin watanni biyu kacal, to muna kallon shekaru biyu masu zuwa da kyakkyawan fata da kuma babban buri, Insha Allah akwai gagarumar tafiya a gabanmu, Ba mu san irin girman abin da Allah zai kai mu gare shi ba, amma muna da yakinin cewa idan muka ci gaba da aiki da gaskiya, jajircewa, ilimi da kyakkyawar niyya, za mu iya ganin abubuwa masu girma a nan gaba.

Babban burinmu shi ne Allah Ya karɓi niyyarmu, Ya taimake mu wajan cimma manufarmu, Ya sanya wannan tafiya ta zama sanadin amfani ga al'umma, musamman wajan bunƙasa ilimi da ƙwarewar matasa a fannonin fasahohin zamani, Fatanmu shine kada Allah Ya bar mu da ƙarfin kanmu. Ya duba niyyarmu da manufar da muke da ita ga al'ummarmu, Ya ba mu hikima, ƙarfin guiwa da ikon sauke amanar da muka ɗauka.

Muna ƙara mika godiyarmu ga Allah (SWT), sannan muna miƙa saƙon godiya ga dukkan ɗalibai, mabiya, malamai, masana, masu ba da shawara, masu goyon baya da duk wanda ya kasance wani ɓangare na wannan tafiya, Muna kuma neman ƙarin Addu'a daga gare ku.

Ku ci gaba da kasancewa tare da mu, domin wannan tafiya yanzu take fara ɗaukar sabon salo.

NOVACHAIN ACADEMY
22/09/2026

SANARWA TA MUSAMMANMuna farin cikin sanar da ɗaukacin al’umma, ɗalibai, abokan hulɗa da masu bibiyar NovaChain Academy c...
20/09/2026

SANARWA TA MUSAMMAN

Muna farin cikin sanar da ɗaukacin al’umma, ɗalibai, abokan hulɗa da masu bibiyar NovaChain Academy cewa, an naɗa Maryam Abbah a matsayin Chief Executive Officer (CEO) na NovaChain Academy.

A matsayinta na CEO, za ta jagoranci harkokin gudanarwa da ci gaban Academy, tare da aiki kafada-da-kafada da sauran shugabanni da tawagar NovaChain wajan tabbatar da manufofin Academy da kuma inganta ayyukanta. Muna fatan za a samu babban sauyi, kasantuwar irin tarihi, horo, jajircewa da ƙwarewar da ta samu a wasu wuraren da ta taɓa yin aiki.

Wannan naɗi wani mataki ne na ƙarfafa tsarin gudanarwa da ci gaban NovaChain Academy a matsayin cibiyar ilimin Blockchain, Web3 da Digital Innovation.

Muna taya Maryam Abbah murna da wannan amana, tare da yi mata fatan samun nasara a sabon matsayinta.

Congratulations, CEO Maryam Abbah. 💙

NovaChain Academy
20/09/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Muna farin cikin sanar da Rabi'u Biyora cewa NovaChain Academy ta karrama sh...
19/09/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Muna farin cikin sanar da Rabi'u Biyora cewa NovaChain Academy ta karrama shi da Full Scholarship (100%) na mutum biyu a matsayin godiya da girmamawa bisa muhimmiyar gudummawar da ya bayar wajen ilmantar da al’umma, gabatar da jawabai da gudanar da karatuka, musamman a farkon tasowar NovaChain.

Wannan kyauta ce ta nuna godiyarmu ga ƙoƙarinka da irin gudummawar da ka bayar.

Muna taya ka murna.

Allah Ya saka da alheri, Ya ƙara maka ilimi da albarka.

https://t.me/NovaChainBA

— NovaChain Blockchain Academy

ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUH📢 KADA A MANTA! SAURA KWANAKI KAƊAN A RUFE REGISTRATION!NovaChain Academy n...
19/09/2026

ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUH

📢 KADA A MANTA! SAURA KWANAKI KAƊAN A RUFE REGISTRATION!

NovaChain Academy na tunatar da duk masu sha’awar shiga shirinmu cewa saura kwanaki kaɗan kacal kafin a rufe registration, domin mu fara karatunmu a ranar 01/10/2026.

Za mu gudanar da horon wata shida (6 months) a fannoni masu muhimmanci da s**a haɗa da:

🔹 Blockchain Technology
🔹 Web3 Development
🔹 Smart Contracts
🔹 Decentralized Applications (DApps)
🔹 Digital Assets
🔹 Decentralized Finance (DeFi)
🔹 Tokenomics
🔹 Artificial Intelligence (AI)
🔹 Digital Security
🔹 Remote Work & Digital Entrepreneurship

🎓 Kada ku bari wannan dama ta wuce ku. Registration zai kasance a buɗe na ’yan kwanaki kaɗan ne, sannan za mu rufe shi domin fara karatu a ranar 01/10/2026.

💰 Kuɗin Registration: ₦10,000

GTBank:
3005358753
NOVACHAIN ACADEMY LTD

Moniepoint:
6999531401
NOVACHAIN ACADEMY LTD

⚠️ MUHIMMI: Kafin ku yi biyan kuɗi, ku tabbatar cewa sunan asusun da ya bayyana shi ne NOVACHAIN ACADEMY LTD.

📲 Bayan biyan kuɗi:
A tura receipt ta WhatsApp zuwa:
07069591722

☎️ Ƙarin bayani:
09135800666

⏳ Kada ka jira gobe. Yi registration ɗinka yanzu domin ka samu damar kasancewa cikin ɗaliban da za su fara karatu a ranar 01/10/2026.

📢 Domin ganin ayyukanmu da ƙarin bayani, ku shiga Official Channel ɗinmu:
https://t.me/NovaChainBA

NovaChain Academy
19/09/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Muna farin cikin sanar da Sunusi Danjuma Ali cewa NovaChain Academy ta karra...
18/09/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Muna farin cikin sanar da Sunusi Danjuma Ali cewa NovaChain Academy ta karrama shi da Full Scholarship (100%) na mutum biyu a matsayin godiya da girmamawa bisa muhimmiyar gudummawar da ya bayar wajen ilmantar da al’umma, gabatar da jawabai da gudanar da karatuka, musamman a farkon tasowar NovaChain.

Wannan kyauta ce ta nuna godiyarmu ga ƙoƙarinka da irin gudummawar da ka bayar.

Muna taya ka murna.

Allah Ya saka da alheri, Ya ƙara maka ilimi da albarka.

https://t.me/NovaChainBA

— NovaChain Blockchain Academy

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Muna farin cikin sanar da Abdul-hadee Isah Ibraheem cewa NovaChain Academy t...
18/09/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Muna farin cikin sanar da Abdul-hadee Isah Ibraheem cewa NovaChain Academy ta karrama shi da Full Scholarship (100%) na mutum biyu a matsayin godiya da girmamawa bisa muhimmiyar gudummawar da ya bayar wajen ilmantar da al’umma, gabatar da jawabai da gudanar da karatuka, musamman a farkon tasowar NovaChain.

Wannan kyauta ce ta nuna godiyarmu ga ƙoƙarinka da irin gudummawar da ka bayar.

Muna taya ka murna.

Allah Ya saka da alheri, Ya ƙara maka ilimi da albarka.

https://t.me/NovaChainBA

— NovaChain Blockchain Academy

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Muna farin cikin sanar da Aliyu Dahiru Aliyu cewa NovaChain Academy ta karra...
18/09/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Muna farin cikin sanar da Aliyu Dahiru Aliyu cewa NovaChain Academy ta karrama shi da Full Scholarship (100%) na mutum biyu a matsayin godiya da girmamawa bisa muhimmiyar gudummawar da ya bayar wajen ilmantar da al’umma, gabatar da jawabai da gudanar da karatuka, musamman a farkon tasowar NovaChain.

Wannan kyauta ce ta nuna godiyarmu ga ƙoƙarinka da irin gudummawar da ka bayar.

Muna taya ka murna.

Allah Ya saka da alheri, Ya ƙara maka ilimi da albarka.

https://t.me/NovaChainBA

— NovaChain Blockchain Academy

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Muna farin cikin sanar da Chizo1Germany cewa NovaChain Academy ta karrama sh...
18/09/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Muna farin cikin sanar da Chizo1Germany cewa NovaChain Academy ta karrama shi da Full Scholarship (100%) na mutum biyu a matsayin godiya da girmamawa bisa muhimmiyar gudummawar da ya bayar wajen ilmantar da al’umma, gabatar da jawabai da gudanar da karatuka, musamman a farkon tasowar NovaChain.

Wannan kyauta ce ta nuna godiyarmu ga ƙoƙarinka da irin gudummawar da ka bayar.

Muna taya ka murna.

Allah Ya saka da alheri, Ya ƙara maka ilimi da albarka.

https://t.me/NovaChainBA

— NovaChain Blockchain Academy

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Muna farin cikin sanar da mahmud galadanci II cewa NovaChain Academy ta karr...
18/09/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Muna farin cikin sanar da mahmud galadanci II cewa NovaChain Academy ta karrama shi da Full Scholarship (100%) na mutum biyu a matsayin godiya da girmamawa bisa muhimmiyar gudummawar da ya bayar wajen ilmantar da al’umma, gabatar da jawabai da gudanar da karatuka, musamman a farkon tasowar NovaChain.

Wannan kyauta ce ta nuna godiyarmu ga ƙoƙarinka da irin gudummawar da ka bayar.

Muna taya ka murna.

Allah Ya saka da alheri, Ya ƙara maka ilimi da albarka.

https://t.me/NovaChainBA

— NovaChain Blockchain Academy

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Muna farin cikin sanar da Aliyu Samba cewa NovaChain Academy ta karrama shi ...
18/09/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Muna farin cikin sanar da Aliyu Samba cewa NovaChain Academy ta karrama shi da Full Scholarship (100%) na mutum biyu a matsayin godiya da girmamawa bisa muhimmiyar gudummawar da ya bayar wajen ilmantar da al’umma, gabatar da jawabai da gudanar da karatuka, musamman a farkon tasowar NovaChain.

Wannan kyauta ce ta nuna godiyarmu ga ƙoƙarinka da irin gudummawar da ka bayar.

Muna taya ka murna.

Allah Ya saka da alheri, Ya ƙara maka ilimi da albarka.

https://t.me/NovaChainBA

— NovaChain Blockchain Academy

Address

Area 11
Abuja

Telephone

+2347037281665

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NovaChain Academy posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to NovaChain Academy:

Shortcuts

Share

Category