04/10/2014
Sallar Idin Layya:
1. Jama'a ina mana barka da salla. Allah ya karbi ayyukanmu na kwarai, ya yafe mana kurakuren mu, ya sanya mu cikin 'yantattun bayinsa. Ameen.
2. Musulmi suna da idi guda biyu da Allah ya zaba musu, a madadin na jahiliyya, su ne Idul Fitr, da Idul Adh'ha. (Muslim #1218).
3. Fita zuwa sallar idi farilla ce, bisa magana ta malamai mafi inganci. (Bukhari #342, Muslim #890).
4. Kuma ana yinta ne bayan rana ta d**o har zuwa zawali, bisa ijma'in malamai.
5. Yana da kyau a yi sammakon yinta, musamman sallar layya, domin mutane su samu damar cin naman layyarsu da wuri. (Bukhari #951). Sabanin idul fitr, ana son jinkirta kadan saboda mutane su samu damar fitar da zakkar fidda-kai.
6. Sunnar Annabi (S.A.W) ita ce yin sallar idi a Filin idi, ba a cikin masallaci ba. (Bukhari #956, Muslim #889). Sai dai idan akwai uzuri kamar ruwan sama to babu laifi a yi ta a masallaci.
7. Yawancin malamai suna ganin cewa, mutanen makka ya fi musu, su yi ta a cikin masallacin Harami, domin akan haka aikin malamai magabata ya gudana.
8. Yana da kyau mutum kafin ya fita idi ya yi wanka ya sanya ti**re, kamar yadda ya tabbata daga aikin Ali da Abdullahi ibn Umar (RA).
9. Mutum ya yi ado da sababbin kayayyaki masu kyau. (Bukhari #948, Muslim #2068). Wannan hukuncin ya shafi maza ne kadai banda mata (Abu Dawud #565, Ahmad #6118).
10. Yana da kyau ya fita yana kabbara. (Baqarah, Aya:185).
11. Kuma ana fita har da 'yammata da tsofaffi da masu al'ada, sai dai masu al'ada za su nisanci wurin sallah. (Bukhari #971, Muslim #890).
12. Sunna ce mutum ya sa6a hanya wajen tafiya da komawa gida idan hakan zai yiwu. (Bukhari #986).
13. Sallar Idi ba ta da nafila a gabaninta ko a bayanta. Sai dai mutumen da ya saba sallatar walaha zi iya sallatarta kafin idi. (Bukhari #989).
14. Liman zai musu salla ba tare da kiran salla ko ikama ba. (Bukhari #960, 961, Muslim #885, 886).
15. Sallar idi raka'o'i biyu ne kacal, bisa ijma'in malamai. (Ahmad #257 Nasa'i #1420, Ibn Majah #1063).
16. A raka'ar farko zai yi kabbara (7) bayan kabbarar harama. A raka'a ta biyu zai yi kabbara (5) bayan kabbarar tsayuwa. (Abu Dawud #1149-1150, Ibn Majah #1280).
17. Kabarbarin nan mustahabbi ne ba wajibi ba, don haka barinsu bisa kuskure ko dagangan ba ya bata salla.. Wannan babu sa6ani akansa a gurin malamai.
18. Babu wani abu da ya zo daga Annabi (S.A.W.) na zikiri tsakanin wadannan kabarbari. Sai dai an samu daga wasu daga cikin sahabbai irin su Ibn Mas'ud, da Abu Musa, da Huzaifa, suna cewa, bayan duk wata kabbara zai yi hamdalah da salati ga Annabi (S.A.W). Wannan shi ne ra'ayin Imam As-Shafi'i, da Ibn Taimiyya. (Baihaqi 3/291).
19. In ya ga dama ya daga hannu tare da kowace kabbara, kamar yadda Ibn Umar yake yi a kabarbarin sallar janaza. In ya so kuma ya bari, saboda rashin tabbatar wani hadisi daga Annabi (S.A.W.) akan hakan. (Al-Mughni 2/120).
20. Mustahabbi ne ya karanta fatiha da suratul A'la a raka'a ta farko, ya karanta suratul Ghashiyat a raka'a ta biyu. (Muslim #878). Ko ya karanta Suratu Q, a raka'a ta farko, da suratul Qamar a raka'a ta biyu. (Muslim #891).
21. Sannan liman ya yi huduba bayan salla. Wannan ijma'i ne na malamai. (Bukhari #961, 962 Muslim #885, 884).
22. Sauraren wannan hudubar mustahabbi ne ba wajibi ba, bisa ijma'in malamai. (Abu Dawud #1155, Nasa'i #1571, Ibn Majah #1290, Al-irwa' #629).
23. An shar'anta yin kabarbari a ranekun idi a ko ina ba wai sai bayan sallolin farilla ba kadai. Babu wani hadisin Annabi (S.A.W) da ya inganta akan hakan. Amma akwai aikin wasu daga cikin sahabbai kamar Ali, Ibn Abbas, Ibn Mas'ud (Allah ya yarda da su), kuma akan hakan ne aikin musulmi ya gudana.
24. Babu wata sigar kabbara ta musamman da ta zo daga Annabi (S.A.W). Amma an samu daga wasu sahabbai kamar Ibn Mas'ud Ibn Abbas da Salman Al-Farisi (Allah ya yarda da su).
25. Yana da kyau musulmi su rika yiwa junansu murnar barka da salla. Kamar yadda aka samu sahabbai suna yiwa junansu, har suna cewa, "Taqabbalallahu Minna wa minka". (Fathul Bari 2/446, Tamamul Minnah, shafi #354).
Allah ya karba mana, ya maimaita mana. Amin.
Daga shafin Dr. Muhd Sani Umar R/lemo... Hafizahullah