14/03/2026
🇷🇺🇮🇷 Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, na shirin ganawa da sabon Jagoran Ƙoli na Iran, Mojtaba Khamenei, karo na farko.
Jakadan Iran a Rasha, Kazem Jalali, ya bayyana a wata hira da kamfanonin labarai na Rasha cewa ana sa ran ganawar farko kai tsaye tsakanin Putin da sabon Jagoran Ƙolin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, za ta iya gudana daga baya a wannan shekarar.
A cewar Jalali, ana sa ran ganawar za ta kasance ne a yayin taron ƙasashen da ke kewaye da Tekun Caspian Sea, wanda Iran za ta karɓi bakuncinsa a ranar 12 ga Agusta, 2026, a birnin Tehran.
Taron zai haɗa shugabannin ƙasashen da ke kewaye da Tekun Caspian, kuma ana ganin zai zama dama ta farko da manyan shugabannin Moscow da Tehran za su yi ganawar kai tsaye tun bayan da Mojtaba Khamenei ya hau kan jagorancin ƙasar Iran.
Har ila yau, Jalali ya bayyana cewa Mojtaba Khamenei mai shekaru 56 yana cikin ƙoshin lafiya, kuma a shirye yake ya jagoranci Iran a wani lokaci da ya ce ƙasar na fuskantar manyan ƙalubale
13/03/2026
Iran Har Yanzu Na Kera Makamai Masu Linzami 100 Duk Wata Duk Da Hare-Haren Da Ake Kai Mata
Duk da hare-haren da ake kaiwa, rahotanni sun nuna cewa Iran har yanzu tana iya kera kusan makamai masu linzami 100 a kowane wata, lamarin da ke ƙara tayar da hankali cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya zama yaki mai tsawo.
Masana sun ce ko da Amurka na ci gaba da kai hare-hare, ikon Iran na sake cika ma’ajiyar makamai nata na iya ba ta damar ci gaba da matsin lamba na soja na dogon lokaci.
Saboda haka, masana suna gargadin cewa wannan rikici tsakanin bangarorin biyu na iya ɗaukar watanni maimakon makonni, idan yadda rikicin ke ƙaruwa a yanzu ya ci gaba.
13/03/2026
Wuta Ta Tashi a Kan Jirgin Ruwa na Yakin Amurka USS Gerald R. Ford a Tekun Red Sea, Sojoji Biyu Sun Ji Rauni
Wata wuta ta tashi a cikin jirgin ruwan yaki na Amurka mai ɗaukar jiragen sama USS Gerald R. Ford (CVN-78), wanda shi ne mafi girma a cikin jiragen ruwan United States Navy, yayin da yake kan aikin sintiri a Red Sea.
Rahotannin farko sun nuna cewa ma’aikatan jirgin biyu sun ji rauni a lokacin da lamarin ya faru. Dukkan sojojin sun samu kulawar likitoci, amma har yanzu ba a bayyana yadda raunukan nasu suke ba.
Jami’an sojin Amurka sun tabbatar da cewa an shawo kan lamarin, kuma jirgin ruwan har yanzu yana aiki yadda ya kamata, yana ci gaba da aikinsa a yankin.
12/03/2026
Shugaban Rundunar Ruwa ta IRGC Ya Ce Dole Jiragen Ruwa Su Nemi Izinin Iran Don Wucewa Ta Hormuz, Ya Kare Harin Kan Jirgin Thailand
Alireza Tangsiri, kwamandan rundunar ruwa ta IRGC (Islamic Revolutionary Guard Corps), ya bayyana cewa dukkan jiragen kasuwanci dole ne su nemi izinin Iran kafin su ratsa Mashigar Hormuz (Strait of Hormuz).
Yayin da yake magana a Tehran a ranar 12 ga Maris, Tangsiri ya sanar da abin da ya kira sabon mataki mai ƙarfi na sarrafa zirga-zirgar ruwa, yana gargadin cewa duk jirgin da ya yi ƙoƙarin wucewa ta mashigar ba tare da izini ba zai fuskanci sakamako.
Shugaban rundunar ruwan ta IRGC ya kuma yi magana kan hare-haren da aka kai kan jiragen kaya uku kwanan nan, ciki har da jirgin Thailand mai suna “Mayuree Naree.” A cewarsa, an zargi jirgin da yin watsi da gargadin Iran tare da ƙoƙarin wucewa ta mashigar, wanda ya sa sojojin Iran s**a tare shi tare da kai masa hari.
Tun bayan rikicin ya ƙara tsananta a ranar 28 ga Fabrairu, an ruwaito cewa akalla jiragen ruwa 14 ne aka kai wa hari a yankin, lamarin da ya ƙara jefa damuwa kan tsaron wannan muhimmiyar hanyar kasuwancin ruwa ta duniya.
A game da jirgin Thailand ɗin, har yanzu ma’aikatan jirgin uku ‘yan Thailand ba a gansu ba. Ana zargin suna makale a cikin ɗakin injin bayan wata mummunar gobara ta tashi a cikin jirgin lokacin harin.
12/03/2026
Iran da kungiyoyin da take goyon baya kamar Hezbollah sun kai hare-hare da makamai masu linzami (missiles) da drones zuwa Israel.
Daily Arewa
09/03/2026
🇫🇷🇮🇷: Emmanuel Macron ya sanar da shirin sake buɗe Strait of Hormuz tare da tsaron jiragen ruwa na haɗin gwiwa.
Faransa ta ce tana shirin gudanar da wani aiki na “tsaro kawai” tare da abokan tarayya don tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma dawo da jigilar mai da iskar gas ta wannan muhimmiyar hanya ta Hormuz.
Birnin Paris zai tura manyan ƙungiyoyin jiragen ruwa, ciki har da jirgin mai ɗaukar sojoji Charles de Gaulle (R91) da kuma wasu frigates da dama a fadin Eastern Mediterranean, Red Sea, da Strait of Hormuz.
Daily Arewa
09/03/2026
🇺🇸🇮🇷 An hallaka ƙarin jiragen ruwa 3 na Iran a cikin Ƙogin Farisa.
Sojin ruwa na Amurka na ci gaba da farautar jiragen ruwa na Iran waɗanda ke a haɗe a tashoshinsu.
09/03/2026
China ta yanke shawarar tura sabbin tech‑drones tare da taimakon Iran
Follow Daily Arewa
09/03/2026
Jiragen Yaƙin Amurka B-52 Sun Sauka a Birtaniya Bayan Rahoton Harin Iran
Jiragen yaƙi uku na B-52 Stratofortress na Rundunar Sojin Sama ta United States Air Force sun sauka a sansanin RAF Fairford bayan sun kammala wani hari na bama-bamai a kan Iran, kamar yadda rahotanni s**a nuna.
An ga jiragen suna sauka a cikin yanayin hazo mai kauri a sansanin da ke United Kingdom, wanda yake zama muhimmin wuri na gaba da Amurka ke amfani da shi domin saukar da manyan jiragen yaƙinta a Turai.
Jiragen B-52 Stratofortress na iya ɗaukar manyan bama-bamai na al’ada da kuma makamai masu linzami masu dogon zango (cruise missiles). Saboda haka, suna daga cikin manyan jiragen da United States ke amfani da su wajen kai hare-haren dogon zango.
Rahoton dawowar jiragen ya zo ne a lokacin da rikicin soja ke ƙara tsananta tsakanin Israel da Iran, yayin da hare-hare da ramuwar gayya ke ci gaba da faruwa a yankin.
Masu nazarin harkokin tsaro sun ce amfani da irin waɗannan manyan jiragen yaƙi masu dogon zango alama ce ta ƙarin tsanantar rikicin, kuma yana nuna yadda manyan kayan aikin soja ke ƙara shiga cikin wannan faɗa.
Daily Arewa
09/03/2026
Jama'a Sun Yi Murna Bayan An Nada Mojtaba Khamenei Sabon Jagoran Addini na Iran
Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa dubban mutane a Iran sun fito kan tituna suna murna bayan Majalisar Kwararru (Assembly of Experts) ta sanar da nada Mojtaba Khamenei, wanda ake kira Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei, a matsayin sabon Jagoran Addini (Supreme Leader) na Iran.
Mojtaba Khamenei shi ne ɗa na biyu ga marigayi Jagoran Addini Ali Khamenei, kuma nadin nasa ya sa ya zama Jagoran Addini na uku tun bayan kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan Iranian Revolution a shekarar 1979.
Ana sa ido sosai kan hawansa wannan matsayi a cikin gida da ma duniya baki ɗaya, domin masu lura da al’amura da dama suna ganin nadin a matsayin wata hanya ta ci gaba da riƙe iko a cikin tsarin siyasa da na addini na ƙasar Iran.
Wannan sauyi ya zo ne a lokacin da ake fama da tashin hankali a cikin ƙasar da kuma yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan ya ƙara muhimmancin wannan sauyin shugabanci a fannin siyasar duniya.
Follow Daily Arewa
08/03/2026
Da ƊUMI-ƊUMI Majalisar Assembly of Experts ta ƙasar Iran ta sanar da cewa Mojtaba Khamenei ne zai gaji mahaifinsa Ali Khamenei a matsayin Babban Jagoran ƙasar.
An haifi Mojtaba Khamenei ne a ranar 8 ga Satumba, 1969 a birnin Mashhad, da ke arewa maso gabashin Iran. Shi ne ɗa na biyu cikin ‘ya’ya shida na Ali Khamenei.
Matsayin Babban Jagora a Iran shi ne mafi girman mukami a tsarin mulkin ƙasar, wanda ke da iko a kan muhimman harkokin siyasa, soja da addini. Sabon rahoton na nuni da yiwuwar sauyi a shugabancin ƙasar nan gaba.
Daily Arewa
08/03/2026
IRGC ta fitar da bidiyon harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila da sansanonin sojin Amurka a zagaye na 28 na “True Promise 4”
Rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta fitar da wani bidiyo da ke nuna harba makamai masu linzami na Kheibar Shekan, Emad, da Ghadr zuwa yankin Israel da kuma sansanonin sojin United States.
A cewar majiyoyin sojin Iran, an bayyana harba makaman a matsayin wani bangare na Operation True Promise 4, musamman a zagaye na 28 na hare-haren da ake kaiwa.
Daily Arewa