31/12/2025
🌐 Menene DNS? | What is DNS?
DNS (Domain Name System) wani tsarin internet ne da yake taimakawa wajen juya sunan website zuwa IP address. Mutane suna amfani da sunaye kamar www.example.com, amma computers da servers suna fahimtar numbers (IP addresses).
DNS yana aiki ne kamar littafin waya (phonebook) na internet. Idan ka rubuta sunan website a browser, DNS ne ke taimakawa wajen nemo inda server ɗin website take, sannan ya haɗa ka da ita cikin sauri.
Misali:
Idan ka rubuta www.example.com, DNS ne ke gano ainihin adireshin IP dinda ke ɗauke da wannan shafin – kamar 12.34.56.78 – wanda kwamfutarka ke buƙata domin ta san inda zata nufa.
Kamar yadda zaka iya rubuta sunan abokinka a waya maimakon tuna lambar sa, haka DNS ke sauƙaƙa mana wajen shiga shafukan yanar gizo wato (Websites).
⚙️ 4 Features na DNS
1️⃣ Name Resolution
DNS yana canza domain name kamar www.example.com zuwa IP address da computer zata iya fahimta.
👉 This makes websites easy to remember.
2️⃣ Speed & Performance
DNS yana taimakawa wajen saurin buɗe websites ta hanyar caching.
👉 Faster loading time for users.
3️⃣ Reliability
DNS servers suna da yawa (distributed). Idan ɗaya ta bar aiki, wata zata yi aiki.
👉 This keeps the internet running all the time.
4️⃣ Security Support
DNS yana taimakawa wajen tsare website, kamar blocking din malicious domains da phishing sites.
👉 Helps improve network security.
10/10/2025