23/09/2025
Wannan cutar haryanzu ba’a gano maganin dake warkar da ita ba
Mutanen dake acikin hatsarin kamuwa da wannan cutar sun haɗa da:
Ma’aikatan kamfanin gidan siminti, ma’aikatan kamfanin sarrafa shinkafa, ma’aikatan t**i, ma’aikatan lebarori masu aikin gini, ma’aikatan gona masu sarrafa gero, dawa, masara, shinkafa, alkama, da dusa zasu iya kamuwa da cutar dake toshe numfashi wato “asthma”
Amfani da takunkumin hanci “face mask” yanada matuƙar amfani agareku musamman alokacin da kuke aiki 📌
—————————————
Asthma cuta ce dake toshe numfashi
Hanyoyin da mutum ke shaƙar iskan numfashi ne zasu kumbura, su toshe, sai kaga mutum yana numfashi acikin wahala da firgici.
—————————————
Abubuwan dake kawo cutar “asthma” sun haɗa da:
1. Gado daga iyaye
2. Mutanen da suke yawan fama da mura batare da shan magani ba ko zuwa assibiti ba
3. Yaran da aka haifa batare da cikar lokacin haihuwarsu ba. Misali yan wata bakwai (7 months baby)
4. Shan taba sigari ko wiwi
5. Yawan shaƙar gurɓatattar iska
6. Ƙiba sosai da girman jiki
7. Da irin ma’aikatan dana lissafa muku a farko daga sama
————————————-
Abubuwan dake kawo toshewar numfashi ga mai cutar asthma sun haɗa da:
Sanyi alokacin hunturu, shaƙar hayaƙi, ƙura alokacin shara, shaƙar ƙamshin turare ko wari, da sauransu.
————————————-
Menene maganin cutar “asthma”
Haryanzu ba’a gano menene asalin maganin wannan cutar ba, amma akwai hanyoyin da ake bi domin sauƙaƙa wannan cutar
1. Ana amfani da inhaler (maganin shaka) don buɗe hanyoyin iska alokacin da s**a toshe.
2. Ana shan magungunan rage kumburin hanyar iskar numfashi don hana tashin wannan cutar
3. Gujewa abubuwan dake tada wannan cutar
————————————-
⚠️ Facebook ba assibiti bane, idan kana fama da cutar toshewar numfashi ko matsalar numfashi kaje assibiti domin samun gwaji da maganin daya dace.
Alhassan Mai Lafia