لا يوم كيومك يا أبا عبد الله...
Thabyeen Channel
Al- Thabyeen Channel tasha ce da aka bude ta domin wayar da kan mutane da kuma ilimantar dasu ta hanya mafi dacewa wajen isar da saƙo.
Wannan tasha tana karkashin Mu'assasar Muntada ne wadda wasu ɗaliban addini dake Najaf suke jagoranta.
25/06/2026
Ashura ta koyar da duniya cewa gaskiya tana rayuwa har abada, ko da masu kare ta sun yi shahada
22/06/2026
Darasin Ashura na Yau
"Mafi haɗarin makiyin gaskiya ba wanda yake yaƙarta a fili ba ne; wanda yake sa mutane su manta da ita ne."
Banu Umayya ba su fara lalata al'umma da takobi ba. Sun fara ne da canza tunani, karkatar da ma'auni, da sanya mutane su saba da abin da bai dace ba har ya zama kamar al'ada.
A yau ma, ba kowane hari ake yi wa addini, ɗabi'a, da gaskiya da ƙarfi ba. Wani lokaci ana kai harin ne ta hanyar nishaɗi marar iyaka, shagaltuwa da abubuwan banza, da rayuwar da ba ta bar wa mutum damar yin tunani kan manufar rayuwarsa.
Ashura tana koya mana cewa mutum zai iya rasa tafarki ba tare da ya shiga yaƙi da gaskiya ba; ya isa kawai ya daina kula da ita.
Saboda haka, ɗaya daga cikin manyan ayyukan mai jiran Imam Mahdi (a.j) shi ne kiyaye farkawar zuciyarsa. Ya kasance yana tambayar kansa:
Me nake rayuwa dominsa?
Wane buri ne yake jagorantar rayuwata?
Shin ina gina kaina ne domin Allah ko domin son zuciya?
Al'ummar da ta manta da manufarta ba za ta iya gina makomarta ba. Kuma zuciyar da ta manta da Allah ba za ta iya ɗaukar nauyin gyaran duniya ba.
"Karbala ba ta koya mana kawai yadda ake mutuwa saboda gaskiya ba; ta koya mana yadda ba za mu rayu cikin gafala har mu manta da gaskiya ba."
Kare hadafin motsin Imam Hussain yafi muhimmanci Kuma wajibi ne!
Akwai darasi me muhimmanci a karshen qissar!
21/06/2026
Darasin Ashura na Yau
"A Karbala, ba duka waɗanda s**a yi yaƙi da Husaini ne s**a ƙi shi ba; da yawa daga cikinsu sun fifita duniyarsu a kansa."
Wannan shi ne ɗaya daga cikin mafi girman darussan Ashura. Matsalar mutane da yawa ba rashin sanin gaskiya ba ce, sai dai rashin shirin biyan kuɗin tsayawa tare da ita.
Umar bn Sa'ad ya san Husaini ɗan Manzon Allah ne. Wasu daga cikin rundunar Kufa sun rubuta wasiƙun gayyata gare shi. Amma lokacin da duniya ta zo a hannu ɗaya, gaskiya kuma a ɗaya hannun, s**a zaɓi duniya.
A yau ma, ba lallai ne mutum ya ƙaryata gaskiya da harshensa ba domin ya yi nesa da ita. Wani lokaci yana saninta, yana son ta, amma yana barinta saboda wata fa'ida, wani matsayi, ko tsoron rasa abin duniya.
Ashura tana tambayar kowane ɗayanmu:
Idan gaskiya ta nemi sadaukarwa daga gare ka, me za ka zaɓa?
Mai jiran Imam Mahdi (a.j) yana koyon wannan darasi tun yanzu. Domin lokacin bayyanarsa ba zai zama lokacin furuci kawai ba, zai zama lokacin gwaji tsakanin maslaha ta kai da kuma nauyin gaskiya.
Saboda haka, duk lokacin da ka fifita ƙa'idarka a kan ribarka, ka fifita amana a kan anfani, ka fifita yardar Allah a kan son zuciya, kana rushe wani ƙaramin Yazidu da ke ƙoƙarin zama a cikin ranka.
"Ba kowane mutum ne yake sayar da gaskiya saboda ya ƙi ta ba; mafi yawansu suna sayar da ita ne saboda sun fi son abin da za su samu idan sun bar ta."
20/06/2026
Darasin Ashura na Yau
"Matsalar mutane da yawa ba rashin sanin abin da ya kamata su yi ba ne; matsalar ita ce jinkirta yin sa har sai lokaci ya wuce."
A Karbala, mutane da yawa sun gane gaskiya bayan an gama komai. Sun yi nadama, sun yi kuka, sun yi tir da abin da ya faru. Amma nadama ba ta canza tarihi. Abin da tarihi yake buƙata shi ne tsayawa kan gaskiya a lokacin da ake buƙatar hakan.
Ashura tana koya mana cewa mafi yawan gwaje-gwajen rayuwa suna da lokacin su. Akwai lokacin magana, akwai lokacin tsayawa, akwai lokacin sadaukarwa. Wanda ya rasa lokacinsa, zai iya gane gaskiya daga baya amma ba zai iya mayar da damar da ta shuɗe ba.
A yau, al'umma tana buƙatar matasa masu ɗaukar nauyi, masu kare gaskiya, masu yada ilimi, da masu gyara kansu da muhallinsu. Ba gobe ba, ba idan komai ya yi sauƙi ba, sai yanzu.
Mai jiran Imam Mahdi (a.j) yana rayuwa da tunanin cewa kowace rana dama ce ta shiryawa. Ba ya cewa "idan na samu lokaci zan gyara kaina"; yana amfani da lokacinsa wajen gyara kansa tun yanzu.
"Darasin Karbala shi ne cewa gaskiya ba ta jiran wanda yake jinkiri; kuma wanda yake son taimakon Imam Mahdi gobe, dole ne ya fara shirya kansa yau."
19/06/2026
Darasin Ashura na Yau
"Babban makamin zalunci shi ne tsoron da yake sanyawa a zukatan mutane; babban makamin muminai kuwa shi ne yaƙinin da yake sanyawa a zukatansu."
Daya daga cikin manyan darussan Karbala shi ne cewa zalunci ba ya rayuwa da ƙarfinsa kawai, yana rayuwa ne da tsoron da yake haifarwa. Yazidu bai nemi biyayya daga mutane kawai ba; ya nemi su ji tsoron ƙin biyayya.
Amma Imam Husaini (a.s) ya koya mana cewa idan zuciya ta cika da yaƙini ga Allah, tsoro ba zai iya mallakar ta ba. Shi ya sa ya tsaya tsayin daka duk da cewa ya san girman haɗarin da ke gabansa.
A yau ma akwai nau'o'in tsoro da yawa: tsoron rasa matsayi, tsoron s**a, tsoron talauci, tsoron zama daban da mutane. Sau da yawa waɗannan tsorukan ne suke hana mutum tsayawa kan gaskiya.
Mai jiran Imam Mahdi (a.j) yana koyon karya waɗannan sarƙoƙin tun kafin bayyanarsa. Domin ba za a iya taimakon jagoran adalci ba da zuciyar da tsoro ya mamaye.
Saboda haka, duk lokacin da ka fifita yardar Allah a kan tsoron mutane, ka faɗi gaskiya duk da wahala, ka kare abin da yake daidai duk da matsin lamba, kana raya ruhin Karbala a cikin ranka.
"Karbala ta tabbatar da cewa idan yaƙini ya shiga zuciya, tsoro zai fita; kuma idan tsoro ya fita, mutum zai zama mai cancantar ɗaukar nauyin gaskiya."
18/06/2026
MASIRAR KARBALA 04
Hakika wanda ya yaƙe ku ya yi Asara Ya Imam
RANAR 03 GA WATAN MUHARRAM
Isowar Umar Bin Sa'ad L.A filin karbala.
Abin da ya faru a 3 ga Muharram 61H bayan isowar Umar ibn Sa'd Karbala shi ne matakin farko na tattaunawa tsakanin Umar bn Sa'ad da Imam Husayn kafin a kai ga rikicewa da yaƙi
Umar bn Sa'ad L.A ya iso Karbala ne tare da rundunar da aka turo shi da ita daga Kufa bisa umarnin gwamnan Kufa Ubaydullah ibn Ziyad L.A
Umar yazo karbala ne tare da manufofi kamar haka:
1. Ya hana Imam Husaini shiga Kufa;
2. Ya tilastawa Imam Husaini A.S yin mubaya'a ga Yazidu L.A;
3. Idan Imam Husaini A.S bai yarda ba, a yi yaƙi.
Wannan sune manufofin da aka baiwa Umar idan yazo ya tabbatar da su, ko kuma ayi yaƙi, tom dama kuma manufar su shine yaƙi din, saboda sun san cewa Imam ba zai taba yi musu mubaya'a ba.
Bayan Umar L.A ya kafa sansaninsa, ya fara aika ƴan sako wurin Imam domin ya fahimci matsayar Imam Husaini A.S.
Tattaunawar farko tsakanin Umar bn Sa'ad L.A da Imam Husaini A.S.
Umar bn Sa'ad ya aika wani mutum zuwa wajen Imam Husaini domin tambayarsa:
"Me ya sa ka zo Kufa?"
Imam Husaini ya bayyana masa cewa:
Na zo ne domin amsa gayyatar da mutanen kufa s**a yi min, bisa wasiku da s**a rubuto min suna gayyatar na zo,
Ba wai nazo ne don na yi mulki ko kuma neman fitina ba,
Amma idan mutanen Kufa ba sa son zuwana, zan iya komawa.
Umar bn Sa'ad L.A ya rubuta wa Ibn Ziyad L.A abin da ya faru tsakanin sa da Imam Husaini A.S.
Ya bayyana masa cewa Imam Husaini A.S yana son ɗaya daga cikin hanyoyi kamar haka:
1. A bar shi ya koma inda ya fito;
2. A bar shi ya je wani wuri daga cikin ƙasar Musulmi;
3. A bar shi ya tafi ya gana da Yazidu L.A
Umar bn Sa'ad ya tattauna da Imam Husaini A.S kai tsaye.
Imam ya yi magana cikin natsuwa.
Sannan yake tuna masa cewa shine Husaini ɗan Aliy dan Fadima Yar Manzon Allah, yayi masa maganganu masu ratsa zuciya.
Sannan Yake kara bayyana masa cewa bai zo domin tayar da fitina ba, ko kuma neman mulki, ya fito ne domin kawo maslaha ga addinin Manzon Allah.
Sannan ya kara bayyana masa cewa idan an ƙi shigar sa kufa tom ya fi masa a barshi ya koma.
Bayan dukkan wannan tattaunawa da ta gudana,
Umar bn Sa'ad L.A ya ji maganganun Imam, kuma ya rubuta wa Ibn Ziyad L.A cewa:
Imam Husaini A.S yana son a barshi ya koma inda ya fito, domin bai fito don tayar da husuma ba.
Martanin Ibn Ziyad L.A
Lokacin da wasiƙar Umar bn Sa'ad L.A ta isa Kufa, Ibn Ziyad L.A bai yarda a bar Imam Husaini A.S ya koma ba.
Ibn Ziyad L.A Ya rubutawa Umar L.A cewa:
1. Dole ne Imam Husaini ya mika wuya;
2. Sannan dole ya yi mubaya'a ga Yazid;
3. Ba za a ba shi damar fita daga ikon gwamnati ba, wato komawa.
A takaice dai dukkan abubuwan da Imam ya nema an hanashi.
A nan ne yanayin ya fara sauyawa daga matakin tattaunawa zuwa takurawa.
A takaice dai ranar 3 ga wata Rana ce ta tattaunawa domin samar da maslaha, bayan zuwan Umar bn Sa'ad L.A, wanda daga ƙarshe dai matsayar da aka cimma shine: Imam Husaini A.S baida damar koma, kuma bashi da damar karisawa kufa.
Assalamu Alaika ya Aba Abdullah
ME YA FARU A RANAR 04 GA WATA?
18/06/2026
ABDULLAHIR RADYY
Ya ƴan uwa muminai...
Yayinda muke ambaton Karbala, ba filin yaƙi da gumurzunta zamu ambata ba kawai, dole zamu ambaci wata makaranta wurin sadaukarwa, da juriya da hakuri da tsayuwa akan Gaskiya.
Wanda tafi shahara da taba zuciya daga cikin su, Kissar Abdullahir Radyy (A.S) wanda shine ƙaramin shahidi a karbala.
Hakika Abdullahir Radyy ya kasance yaro wanda shayar da shi akeyi (jariri)
Be dau takobi ba, sannan beyi musharaka wurin yaki ba, sannan beda wani laifi face kasancewar dan Imam Hussain (A S) .
Bayan an hana Imam Hussain da iyalansa da sahabbansa ruwa tsawan ranaku ya shiga cikin matsanancin kishin ruwa.
A wannan yanayin ne Imamul Hussain (A.S) ya dau Abdullahir Radyy zuwa waɗannan mutanen, Yace musu -ma'anar maganar sa-
Idan har bazaku tausaya min ba toh ku tausaya wa wannan yaron mana, koda kurbi na ruwa ku basa.
Se dai zuciyar data bushe, da idanun data makance daga ganin gaskiya, taky amsa wannan kira na mutumtaka.
Umar dan Sa'ad yay umurni ga harmala dan kahil asadi(L.A) ya harbi jaririn seya harbe sa da kibau me baki uku, harbin sa be sabawa abin harinsa ba ya sauka a wiya me tsarki, a wannan lokacin ne Abdullahir Radyy yay shahada a hannun baban sa (A.S).
Ya ƴan uwa masoya...
Wani irin lefi ne wannan yaron yay?
Shin har yanzu akwai wani uzuri da yarage gahme ikirari cewa abinda ya gudana a karbala kawai yakin siyasa ne? Lallai kisan jinjirin yaro yana bayyana hakikanin zaluncin da Imam Hussain (A.S) ya fuskanta, tabbas Abdullahir Radyy ya zama ramzi na waɗanda aka zalunta, kuma dalili akan me zalunci idan ya rasa mutumtakar sa baya bambance tsakanin mayaki dana goye, ballantana yaro da babba.
Daga nan ne zamu fahimci fitar Imam (A.S), bata kasance dan neman mulki ko wani abu makamancin saba, face dan kariya ga addini da tsayuwa akan insaniyya da karamar mutum.
Muna rokon Allah ta'alah ya azurtamu da ceton Imamul Hussain da iyalansa(A.S), ya sanyamu daga cikin masu riko da hanyasu ya bamu sabaty akan wilayar su.
Click here to claim your Sponsored Listing.