Dr. Murtala Abu-khadeejah

Dr. Murtala Abu-khadeejah Herbal Medical Consultant, Islamic & Prophetic Medicine practitioner, Chine Traditional Doctor.

A tutor, teacher, graphic designer, Content and Digital expert,Tech Skilled personnel.

20/08/2026
20/08/2026
20/08/2026

Za a gudanar da gasar ne a watan Nuwamba, kuma ɗaliban sun samu wannan damar ne bayan da s**a lashe gasar ta ƙasa da aka gudanar a Najeriya.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/4if5BB9

19/08/2026

ARBA'UNA 74
Masallacin marigayi Alhj Yahaya makera

17/08/2026

ARBA'UNA 46
Masallacin inuwa

17/08/2026
MA'ANAR CIWON VARICOCELE DA ABUNDA YA KUNSA DA ABUNDA YA SHAFESHI.DAGADR. ABU-KHADEEJAH 08063053652Wani yayimun tambaya ...
16/08/2026

MA'ANAR CIWON VARICOCELE DA ABUNDA YA KUNSA DA ABUNDA YA SHAFESHI.

DAGA
DR. ABU-KHADEEJAH 08063053652

Wani yayimun tambaya k**ar haka: Menene varicocele? Idan na fahimta yanada banbanci da thrombosis??
Sai na bashi amsa k**ar haka:
Varicocele wata matsala ce da ke faruwa idan jijiyoyin da ke cikin maraina (sc***um) s**a faɗaɗa kuma s**a kumbura, k**ar yadda jijiyoyin ƙafa (varicose veins) suke kumbura.
Ka gane?

Menene alamomin ta?
Alamominta na iya haɗawa da:
Jin nauyi ko ciwo a maraina, musamman idan an daɗe ana tsaye.
Kumburi ko ganin jijiyoyi sun yi k**a da "jakar tsutsotsi" (bag of worms).
Ɗaya daga cikin ƙwayoyin maniyyi (galibi ta hagu) na iya zama ƙarami.
Wasu ma ba sa jin wata alama kwata-kwata.

WASU DAGA ABUBUWANDA YA KAMATA KA/KU SANI AKANTA:
Matsalolin Wannan matsala ta ciwo da zai iya haifarwa:
Rage ingancin maniyyi.
Wahalar samun haihuwa (infertility).
Rage girman ƙwayar maniyyi.

Yadda ake gano shi: Likita zai duba maraina ta hanyar gwaji na jiki, kuma wani lokaci ana yin gwajin ultrasound don tabbatarwa.

Magani:
Idan ba ya haifar da ciwo ko matsalar haihuwa, wani lokaci ba sai an yi magani ba.
Idan yana haifar da ciwo ko matsalar haihuwa, likitancin zamani sunayin tiyata, mu kuma muna bin hanyoyi ne na rufe jijiyoyin da s**a kumbura, ma ana sassauta su dakuma kokarin sun dawo normal.

Idan kana da ko wanda kakeso kar6awa magani yanada kumburi, ciwo, ko yana fuskantar matsalar samun haihuwa, yana da kyau ka ku fada awurin bayani domin a duba ka.
Ku nemeni idan kuna bukatar magani inshaAllah. Fatan an ilmantu? Ngd

Dr. Abu-khadeejah
08063053652
Ngd

Ma'anar THROMBOSIS, kashe kashensa, alamominsa, abubuwan da ke kawoshi, Rigakafi duk atakaice.Rubutawa: Dr. Abu-khadeeja...
16/08/2026

Ma'anar THROMBOSIS, kashe kashensa, alamominsa, abubuwan da ke kawoshi, Rigakafi duk atakaice.
Rubutawa: Dr. Abu-khadeejah 08063053652,
Shugaban cibiyar: ABU-KHADEEJAH CENTRE FOR HERBAL MEDICAL STUDY AND THERAPY
Thrombosis na nufin samuwar gudan jini (blood clot/thrombus) a cikin wata jijiya ko artery a cikin jiki, wanda zai iya rage ko toshe zirga-zirgar jini.
Nau’ukan thrombosis
1. Venous thrombosis – gudan jini ya samu a cikin jijiya mai dawo da jini zuwa zuciya.
Mafi shahara: DVT (Deep Vein Thrombosis), wanda yawanci yake faruwa a cikin ƙafa ko cinyar mutum.
2. Arterial thrombosis – gudan jini ya samu a cikin artery da ke kai jini zuwa gabobi.
Zai iya jawo heart attack ko stroke, gwargwadon inda ya faru.

Alamomin DVT
Kumburin ƙafa ɗaya
Ciwon ƙafa ko mara
Ƙafar ta yi ɗumi
Kalar Ja ko canjin launin fata
Jin nauyi ko matsewa a ƙafar.

Me ke iya haddasa shi?
Muhimman abubuwa sun haɗa da:
Dogon zama ko kwanciya ba motsi.
Tafiya mai tsawo
Bayan tiyata ko rauni
Wasu cututtuka
Kiba
Shan taba
Ciki
Wasu magunguna/hormones
Wasu cututtukan da ke sa jini ya fi saurin yin clot.

Me ya sa thrombosis yake da haɗari?
Babban haɗarin DVT shi ne clot ɗin ya ware daga jijiyar ƙafa ya bi jini zuwa huhu. Wannan ana kiransa pulmonary embolism (PE) kuma yana iya zama barazana ga rai.
Alamomin gaggawa (emergency): wahalar numfashi kwatsam, ciwon ƙirji, tari da jini, bugun zuciya da sauri ko suma → a nemi emergency medical care nan da nan.

Magani:
Maganin thrombosis ya danganta da inda clot yake da girman haɗarinsa. A DVT, likita yakan yi amfani da anticoagulant domin hana clot girma da hana sababbin clots. Jiki ne yake narkar da clot a hankali; ba wai Warfarin yana narkar da shi kai tsaye ba.

A takaice:
Thrombosis = gudan jini da ya samu a cikin jijiya/artery, wanda zai iya toshe zirga-zirgar jini. Mafi hatsarin sa shi ne clot ya tafi huhu (PE), ko ya toshe jini zuwa zuciya ko kwakwalwa.

MAGANINSA
Bayan bincike dakuma gwaji, muna hada maganinsa, kuma ana warkewa da izinin Allah.

Dr. Abu-khadeejah
08063053652

Address

Abuja

Telephone

+2348067080655

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr. Murtala Abu-khadeejah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share