Your Knowledge Companion

Your Knowledge Companion

Share

We share weekly videos to help you utilize technology effectively for personal and educational growth.

11/07/2023

A Bittersweet Farewell to Your Knowledge Companion

Dear friends and followers,

It is with a heavy heart that I write this message today. After much contemplation and reflection, I have made the difficult decision to discontinue my weekly Your Knowledge Companion video tutorials.

Over the past 10 months, it has been an incredible journey filled with learning, growth, and immense support from all of you. I am truly grateful for the love and appreciation you have shown me throughout this time. Building a community of nearly 20,000 followers has been a tremendous honor, and I cherish the connections we have made.

However, as much as I have enjoyed sharing valuable tips and tricks with you, it has become increasingly challenging to sustain this commitment. Creating each video requires an enormous amount of time and energy, from research to editing. As a full-time lecturer with research obligations and other side projects, I have reached a point where I need to prioritize my other responsibilities.

But don't worry, my journey with knowledge-sharing is far from over. Instead of the weekly tutorials, I will be focusing on delivering free lectures on important and timely topics that I believe are crucial for our intellectual growth. Just like the recent lecture on Plagiarism and the one I conducted three months ago on Chatgpt, I will continue to provide thought-provoking discussions to keep our minds engaged.

Furthermore, I want to assure you that the videos I have created will still be accessible through other channels. While they may have a different style, I believe you will continue to find valuable content and inspiration from those sources. My unique approach may be missed, but I trust that the knowledge and positivity will still resonate with you.

Thank you all for your unwavering support, encouragement, and engagement. Your presence has meant the world to me, and I am truly grateful for the trust you have placed in me. As I embark on this new chapter, I humbly ask for your continued support and prayers.

May we all continue to grow in knowledge and wisdom. Stay curious, stay passionate, and always seek the truth.

With heartfelt gratitude.
Malam Daha Tijjani

11/07/2023

Bankwana ba don anso ba, da shirin ku mai farin jini "Your Knowledge Companion"

Ya ku 'yan uwa, abokan arziki da masu bibiya ta,

Cikin alhini da damuwa nake rubuto muku wannan sako a yau.
Bayan nazari mai zurfi da nayi tare da yin tuntuba, na dauki wannan mataki mai tsaurin gaske, wato shawarar daina gudanar da shirin da na saba kawo muku na mako-mako a kafafen sada zumunta wanda ke koya muku Ilimi kan harkokin fasahar sada zumunta mai taken: "Your knowledge Companion".

Cikin watanni goma da nayi tare da ku, ba abin da zan ce sai godiya, domin na tsinci alheri, farin ciki da annashuwa.
Ina alfahari da hadin kan da kuka bani da kuma irin tarin ilimi, bunkasa da muka samu baki dayan mu, cikin watanni goma da da muka yi, muna musayar nazari kan al'amuran da s**a shafi fasaha game da kafafen sada zumunta.

Har Ila yau, Ina matukar godiya gare ku baki daya, saboda kun nuna mini kauna tsawon wannan lokaci. A wannan zamani, samun dama mutum ya hada kan al'umma masu mabanbantan ra'ayi, akida, fahimta har sama da dubu 20 su rika bibiyar sa, ba karamar nasara ba ce, kuma abin alfahari ne. Ina matukar alfahari da wannan alaka da ta kullu tsakanin mu cikin wannan wa'adi.

Kamar yadda nake jin dadin musayar nazari da Ilimi tare da ku kan hanyoyi da dabaru na fasahar zamani da al'amuran soshiyal midiya, a zahiri lamari ne da ke da matukar wahalar ci gaba da dorewarsa. Kirkirar kowanne faifan bidiyo da nake yi yana matukar cinye mini lokaci, k**a daga kan bincike zuwa kan tacewa wato editing na faifan bidiyon. Saboda haka, a matsayina na malamin jami'a wato Lakcara wanda babban aikina na farko mafi muhimmanci shine yin bincike wato Research da kuma wasu al'amuran na koyo da koyarwa da s**a wajaba, na kai lokacin da wajibi ne gare ni in mai da hankali kan wasu muhimman ayyuka da s**a wajaba akai na.

Amma duk da haka, Ina kwadaitar da ku cewa, ku kwantar da hankalin ku, dawainiyar da nake yi na musayar nazari da Ilimi da ku ba wai shikenan an daina ba kenan har abada. Maimakon wancan tsarin na mako-mako, yanzu, na yanke shawarar zan rika gabatar muku da mukala/lakca kan wani al'amari dake kan gaba, ko mafi muhimmanci ga al'umma a lokacin. Ina da kwarin guiwa wannan tsarin zai taimaka gaya wajen yada ilimi da nazari tsakanin al'ummar mu.

Misali, k**ar wannan lakca da na gabatar kwanan-nan kan satar fasaha, ilimi, ko ayyukan wani ka mayar da su naka wato "Plagiarism" da kuma lakcar da na gabatar watanni uku da s**a gabata, kan fasahar Chatgpt, zan ci gaba da bijiro da darussa da dama wadanda a ko da yaushe, za mu kasance ni daku cikin nazarin ilimi.

Bugu da kari, Ina shaida muku cewa, faifan bidiyo da na gabatar da su a shirye-shiryen da muka yi a baya, za su ci gaba da kasancewa a wasu kafafen na sada zumunta, sai dai watakila a iya samun canji wajen gabatar wa da kuma tsari amma Ina yi muku albishir za ku ci gaba da amfana da samun bidiyoyi da za su amfanar da ku, duk da cewa tsarin gabatar da shirin zai sha banbam da wancan amma ina da tabbacin cewa za ku amfana da Ilimin da ke cikin sa.

Ba zan gushe ba, zan ci gaba da mika sakon godiya gare ku baki daya, saboda hadin kai da goyon baya da kuka rika bani. Kasancewa tare da ku babban abin alfahari ne gare ni, naji dadinsa sosai, Ina kara godiya gare ku saboda aminta da kuka yi dani kan wannan namijin kokari. Yayin da nake kokarin shiga sabon tsari a wannan kafa, Ina mika kokon bara da sake neman addu'oi da hadin kai daga gare ku.

Allah ya sa mu ci gaba da amfana da bunkasa tare kan harkokin nazarce-nazarce, ilimi da hikima. Ku dai ku ci gaba da dagewa don neman sani, sannan a kullum kuyi kokarin sanin gaskiyar lamari.

Godiya mai tarin yawa.
Naku, Malam Daha Tijjani

09/07/2023

OUR TUTORIAL ON PLAGIARISM STARTS IN 15 MINUTES

09/07/2023

📢 Announcement: Tutorial on Plagiarism 📚
Join me for an insightful tutorial on plagiarism! It's a must-attend session for students, researchers, and anyone interested in upholding academic integrity. Here are the agenda items we'll cover:
🔹 What is plagiarism? Understand the different forms and consequences.
🔹 Examples of plagiarism to enhance your understanding.
🔹 Exploring self-plagiarism and its implications.
🔹 A comprehensive guide on using the Turnitin platform to check similarity index.
Don't miss out on this valuable opportunity to enhance your knowledge and prevent unintentional plagiarism. Whether you're a student or professional, this tutorial will equip you with essential tools to maintain academic integrity.
📅 Date: 09/07/23
⏰ Time: 1:30 PM
📍 Venue: Zoom (MeetingLink 🙂 https://rb.gy/fm0bs (Passcode: 404688)
Invite your friends and colleagues who might benefit from this tutorial. Let's ensure that our academic work reflects our originality and dedication. See you all there!
Please note: This tutorial is provided Pro Bono (free of charge) as a way of giving back to the community.

Join our Cloud HD Video Meeting Zoom is the leader in modern enterprise video communications, with an easy, reliable cloud platform for video and audio conferencing, chat, and webinars across mobile, desktop, and room systems. Zoom Rooms is the original software-based conference room solution used around the world in board, confer...

06/07/2023

Babbar hanya mafi bullewa da za ku bi don kare Facebook account din ku daga sharrin masu kutsen Internet.
A halin da ake ciki yanzu, tabbatar da cewa Facebook account din ka ya samu cikakken tsaro, ya tsira daga sharrin batagari masu kutse, ba karamin aiki bane. Munin lamarin ma ya kai yanzu, mutum sai ya rasa wanne ne daga cikin kafofin sada zumunta na Internet ya ke da tsaron da hankalin mai amfani da shi zai kwanta sak**akon yadda ayyukan masu kutsen Internet ya zama ruwan dare gama duniya.
Amma duk da haka muna da hanyoyin da za mu bi don dakile wadannan matsaloli har ma mu bai wa Facebook account din mu da sauran account da muke da su a kafofin sada zumunta na zamani/soshiyal midiya kariya daga harin masu kutse. Za mu iya bai wa Facebook account din mu da sauran shafukan mu na soshiyal midiya kariya ta hanyar tsara lambobin sirri (password), masu tsauri da wuyar sha'ani. Sannan canja password din akai-akai, daina hada wayarka da wata waya don amfani da Datar wayar wani ko shi ya yi amfani da ta ka wayar, ( Wi-Fi Hotspots), haka zalika, ku guji shiga duk wani link na website da aka turo muku ta WhatsApp, Facebook ko Email da sunan cewa, in kuka shiga za ku samu wata garabasa, hakan zai taimaka gaya wajen yaki da tsagerun Internet.
Bugu da kari, sak**akon yadda lamarin kutsen yayi yawa jama'a da dama na kokawa kan yadda ake samun bayanansu na sirri, har a yada su. Munin lamarin shi ya sanya jama'a s**a fara neman mafita, har s**a fara daukar matakan da na lissafa su a baya.
Amma fa wannan ba yana nufin jama'a gaba daya ne suke daukar matakan ba, akwai wasu wadanda har yanzu sun yi kunnen uwar shegu shi ya sa suke ta fadawa tarkon tsagerun Internet da ke kutse wa jama'a a kafafen sada zumunta na zamani.
A mukalar yau, zan yi bayani ne dalla-dalla kan muhimmin matakin da za ku dauka don kare Facebook account din ku daga harin masu kutsen Internet (Hackers). Wannan muhimmiyar hanyar da za ku bi don kare Facebook account din ku kuwa, ita ce, kuyi tsarin da ake cewa, "Two Factor Authentication" da turanci.
Wato shi wannan tsari na Two Factor Authentication, wani tsari ne da ba wai kawai lambobin sirri (password), kake bukata ba don shiga Facebook account din-ka, a,a, sai an maka wani gwajin na daban, kafin a tabbatar da cewa, kaine wanda ka mallaki Facebook account din. Yadda lamarin ke faruwa kuwa shine; bayan ka kammala matakin saka lambar sirri (password), website na Facebook zai turomaka da sako dauke da wasu lambobi da ake cewa OTP ta email din-ka ko lambar wayarka, idan ka saka lambobin da aka turomakan ne to shikenan sai a amince maka ka shiga Facebook account din-ka. Wannan na nuna cewa, ko da mutum ya samu lambobin sirrinka (Password) da sunanka (Username), ta wata hanyar ba zai iya shiga ko kwace maka Facebook account din-ka ba.
Abin sha'awar ita ce, saita wannan tsari na Two Factor Authentication yana da matukar sauki, babu wahala ko kadan.
Yadda za ka saita shi kuwa shine k**ar haka: Da farko za ka shiga bangaren tsaro wato security na Facebook account din-ka ko Fejinka, sai kuma ka shiga sashen saiti wato Setting.
Za ka ma iya kallon yadda ake saitawa ta cikin wannan faifan bidiyo...
Haka kuma yana da kyau a koyawa jama'a yadda za su kaucewa wasu hanyoyin fadawa tarkon tsagerun Internet masu kutse. Alal misali, idan kai mutum ne mai ta'adar nan ta amfani da lambar sirri (Password) guda daya a dukkannin shafukan ka/account din-ka, mai kutsen Internet zai iya samun damar kwace maka su gaba daya idan ya samu lambar sirrinka (Password). Don kaucewa fadawa tarkon masu kutse, abin da za ka yi shine; ka guji amfani da lambar sirrinka (Password), iri daya a dukkannin shafuka/account din ka, ka kasance mai amfani da lambobin sirri wato Password kala-kala. Sannan lambobin kar su kasance masu saukin fahimta. Har Ila yau, ya k**ata kai mai amfani da kafar sada zumunta na zamani/soshiyal midiya ka kwana da sanin cewa, yin "Two Factor Authentication" wajibi ne gare-ka, ba wai zabi bane. Wani hanzari ba gudu ba, ya k**ata kusan cewa, yayin da yin"Two Factor Authentication" ya zama sahihiyar hanyar bai wa Facebook account da sauran shafukan sada zumunta na zamani kariya daga sharrin masu kutsen Internet, a bangare guda zai iya kasancewa babbar barazana ga mutumin da bai san yadda zai yi amfani da shi ba. Misali, masu kutsen Internet za su iya amfani da wata fasaha ake cewa "social engineering" inda za su yaudari mutum ya turo musu da cikakkun bayanansa na sirri, musamman lambobin OTP.
Yana da matukar muhimmanci kusan cewa kuskure ne babba, ku bai wa wani lambobin OTP da aka turo muku.
Daga karshe, idan har lambobin OTP dinka ana turo maka su ne ta lambar wayarka, to wajibi ne ka kula da layinka/sim card dinka sosai, domin in ka rasa shi, dai-dai ya ke da ka rasa Facebook account din-ka, sai dai in kana da wani tsari na biyu wato kayi amfani da email din-ka a matsayin jiran ko ta kwana.

29/06/2023

🔥 Amazing Deal Alert! 🔥
💻 SmarPLS Lifetime License for Sale
💰 Price: NGN 20,000 Naira
🚀 Fastest fingers only!
Remote installation is available from anywhere.
If you're looking to harness the power of SmartPLS for your research or data analysis needs, this is your chance to grab this incredible software at a fraction of the original cost. 🎉
Don't miss out on this incredible opportunity! Message now to secure your license. ⏳💡

27/06/2023

Me ake nufi da Artificial intelligence kuma menene makomar-sa?

Artificial intelligence, wata fasaha ce wadda ta ke iya kwaikwayon halayyar Dan Adam. Za a iya fassara Artificial intelligence da duk wani nau'in kwamfyuta wadda aka tsara-ta, za ta iya kwaikwayon wasu halayya na Dan Adam. A wannan zamani yanzu haka ana amfani da ita a bangarori daban-daban a masana'antu, k**ar masana'antun bangaren kiwon lafiya, tallace-tallace, harkokin mulki da gudanarwa da sauransu. A wannan mukala, za mu tattauna ne akan nau'ikan fasahohi daban-daban na Artificial intelligence (Ai), da kuma yadda al'umma za su shirya don rungumar wannan sabon sauyi na fasaha domin tafiya dai-dai da zamani.

Ga yadda Artificial intelligence, ya ke.

A duk lokacin da aka tashi magana aka Artificial intelligence (AI), akan yi zantuttuka masu yawa, amma kuma ba ayin cikakken bayani (gamsashshe) da jama'a za su fahimta. Shin Artificial intelligence na nufin kawai wata na'ura ce da take kwaikwayon halayyar Dan Adam? Ko kuma wani abu ne kawai kirkirarre mai wuyar sha'ani da ake mai kallon mujiya cikin Tsuntsaye?

A wannan mukala, za mu yi kokari mu yi bayani dalla-dalla a fayyace, yadda za mu gamsar da masu sauraronmu, su fahimci me ake nufi da Artificial intelligence. Za mu duba tarihinsa da kuma makomarsa anan gaba.

Me ake nufi da Artificial intelligence?

Artificial intelligence.

Artificial intelligence, wata fasaha ce da ta ke da fadin gaske tana kuma da kananan rassa da kuma hanyoyi daban-danan. Sai dai babbar manufar wannan fasaha ita ce kirkirar wani tsari na koyo tare da sanya na'ura mai kwakwalwa ta iya kwaikwayo ko gudanar da wasu ayyuka da Dan Adam ya ke yi.

Akwai hanyoyi masu yawa da mutum zai iya kirkirar wannan tsari na Artificial intelligence.
Daya daga cikin Irin wadannan hanyoyi shine amfani da na'ura mai kwakwalwa/ inda za ka sa kwamfyuta ta koyi wasu abubuwa ko halayyar Dan Adam wato Machine learning. Idan har akwai isassun bayanai, na'ura mai kwakwalwa wato kwamfyuta tana iya gane wani tsari na fayyace abu da aka dorata akai ko hasashen wani abu da ake kyautata zaton zai faru. Wannan tsari an gwada shi sosai kuma an samu nasara, yana aiki k**ar yadda ya k**ata. Wannan kuma ya faru ne saboda ci gaba da aka samu wajen sabbin na'ura masu kwakwalwa da ake kerawa da kuma bayanai da aka cusawa kwamfyutocin.

Wani bangare na yadda ake amfani da Artificial intelligence shine ta hanyar wasu dalilai masu alamomi. Wannan ya kunshi shiryawa na'ura mai kwakwalwa/kwamfyuta wasu muhimman ka'idoji wanda hakan zai taimakawa kwamfyutar samun damar nadar wasu bayanai da aka riga aka cusa-su a cikin manhajar kyamfyuta. Wadannan hanyoyi sune na farko-farko kuma sun yi farin jini sosai a shekarun baya, amma a yanzu sak**akon sauyin da aka samu da kuma ci gaba a manhajar koyi da kanka, al'amura sun wuce haka.

Wasu muhimman matsaloli ne ake iya magance su ta hanyar amfani da Artificial intelligence?

Akwai muhimman matsaloli masu yawa wadanda ake amfani da Artificial intelligence wajen magance su. Daya daga cikin muhimman su shine yadda za ka sanya na'ura mai kwakwalwa/kwamfyuta ta rika yin wasu halayya ko kwaikwayon wasu halayya na Dan Adam tare da daukar mataki kan wani lamari k**ar yadda Dan Adam ke yi. A zahiri wannan babbar matsala ce mai wuyar sha'ani, saboda wannan tsari na bukatar kwamfyutoci su fahimci al'amuran duniya baki daya tare da iya tuna abubuwa da s**a faru a baya.

Wani muhimmin sashe na wannan fasaha na Artificial intelligence kuma shine, yadda za a iya sanya na'ura mai kwakwalwa)/kwamfyuta ta rika mu'amala da Dan Adam ta hanyar yin magana k**ar yadda shi Dan Adam din ya ke yi, Ba shakka wannan yana da wahala sosai saboda akwai bukatar sanya kwamfyuta ta fahimci yarurruka/harsuna da al'adu na Dan Adam.

Daga karshe, wata muhimmiyar matsala da Artificial intelligence ke iya magance wa kuwa, ita ce, yadda za a iya sanya kwamfyuta/na'ura mai kwakwalwa ta iya kammala wasu ayyuka ko gudanar da wasu ayyuka masu dumbin yawa a lokaci guda. Wannan kuwa sun hada har da; yadda kwamfyutar za ta iya sarrafa/tuka mota ko jirgi ba tare da taimakon Dan Adam ba. Wannan kuwa babbar matsala ce mai wuyar sha'ani saboda ana bukatar na'ura mai kwakwalwa/kwamfyuta ta iya koyo cikin hanzari tare da gaggauta tuna wasu wasu muhimman abubuwa a lokacin da ta ci karo da wani sabon al'amari ko aka shiga cikin hatsari ko neman taimakon gaggawa.

Ya zan yi amfani da wannan fasaha ta Artificial Intelligence?

A rayuwar ka a wannan zamani, za ka iya amfani da fasahar Artificial intelligence ta hanyoyi masu yawa. Misali, za ka iya amfani da dabarar tsara na'ura mai kwakwalwa/kwamfyuta ta rika aiki irin na masinja ko Dan aike ko k**ar yadda manhajar Amazon Alexa ko Apple's Siri su ke yi wajen gudanar da ayyuka k**ar su; sanya maka kade-kade da raye-raye don nishadinka a lokacin da kake bukata, saita maka alarm na waya don tunasar da kai wani aiki da kakeson yi nan gaba a wani lokaci, ko kuma tayar da kai daga bacci da sauransu, da kuma amsa tambayoyi. Haka zalika, za ka iya amfani da fasahar Artificial intelligence wajen yin ayyuka irin su: yin kasafi, motsa jiki don kasancewa cikin koshin lafiya ako da yaushe da kuma koyon sabbin harsuna.

A rayuwar ka, akwai hanyoyi masu yawa wadanda za ka iya amfani da fasahar Artificial intelligence. Alal misali, za ka iya amfani da fasahar Artificial intelligence ka rika mu'amala da abokan huldarka na kasuwanci ko kamfani ba tare da kai ka tattauna da su kai tsaye ba. Wannan tsari zai faru ko kana kusa ko kuma bayan ka fita. Haka kuma za ka iya amfani da hikimar tsara kwamfyuta ta rika mu'amala da abokan huldarka ta hanyar manhajar chatbots a website dinka ko a ofishinka wanda zai rika tattauna kai tsaye da abokan huldarka. Hakan zai rage maka kashe kudi sosai musamman tun da baka dauki ma'aikaci da zai yi wannan aiki ba.

Yanzu dai ina fata ka fahimci yadda wannan fasaha ke aiki tun da ai kunga hanyoyi masu yawa da mutum zai iya amfani da fasahar Artificial intelligence. Kuma fa kunsan ita fasaha kullum ci gaba ake samu, saboda haka za ku ci gaba da ganin sabbin hanyoyi nan gaba da za ku ci gajiyar fasahar Artificial intelligence.

To yanzu me za mu yi idan aka kai wani lokacin da fasahar Artificial intelligence ta kai matsayin da tafi Dan Adam basira?

Idan har aka kai lokacin da Artificial intelligence ya fi Dan Adam basira, tabbas za a ga tasirinsa cikin al'ummar-mu. Wajibi ne muyi tunani akai-akai a matsayin mu na 'yan Adam, kan yadda muke mu'amala da kayayyakin fasaha na zamani.

Akwai abubuwa da dama da ake tsammanin za su iya faruwa idan ta kai ta kawo fasahar Artificial intelligence ta zarce basira da hikima da Dan Adam ke da su. Daya daga cikinsu kuwa shine Artificial intelligence zai zama bawan-mu inda shi za mu sanya ya rika yi mana dukkannin ayyukan da ya k**ata ace mu za mu yi da kan mu. Sai dai a bangare guda Artificial intelligence zai kuma iya zama mana ubangida saboda yawan dogara da za mu yi da shi, zai sa ya zama shi ke juya-mu shine ubangidan-mu, ko kuma mafi muni shine Artificial intelligence zai iya kasancewa kishiya ga Dan Adam, yadda zai rika rayuwa kafada-da-kafada da Dan Adam, ya samar da wata al'umma wadda take da al'adarta na zamantakewar rayuwa.

Ko ma dai me ya faru, a zahiri fasahar Artificial intelligence ta kawo wani babban sauyi a zamantakewar rayuwar bil'adama. Dole ne mu saba da rayuwa a duniyar da na'urar zamani za ta fi Dan Adam basira da hikima. Tabbas babban kalubale ne, wanda dole mu tashi tsaye domin tunkararsa.

21/06/2023

Yadda ake editing sakon WhatsApp

16/06/2023

Yadda ake yin screenshot a computer

04/06/2023

Yadda ake cire background a bidiyo

Want your school to be the top-listed School/college in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address

Abuja, Gwarinpa
Abuja
900108