06/07/2023
Babbar hanya mafi bullewa da za ku bi don kare Facebook account din ku daga sharrin masu kutsen Internet.
A halin da ake ciki yanzu, tabbatar da cewa Facebook account din ka ya samu cikakken tsaro, ya tsira daga sharrin batagari masu kutse, ba karamin aiki bane. Munin lamarin ma ya kai yanzu, mutum sai ya rasa wanne ne daga cikin kafofin sada zumunta na Internet ya ke da tsaron da hankalin mai amfani da shi zai kwanta sak**akon yadda ayyukan masu kutsen Internet ya zama ruwan dare gama duniya.
Amma duk da haka muna da hanyoyin da za mu bi don dakile wadannan matsaloli har ma mu bai wa Facebook account din mu da sauran account da muke da su a kafofin sada zumunta na zamani/soshiyal midiya kariya daga harin masu kutse. Za mu iya bai wa Facebook account din mu da sauran shafukan mu na soshiyal midiya kariya ta hanyar tsara lambobin sirri (password), masu tsauri da wuyar sha'ani. Sannan canja password din akai-akai, daina hada wayarka da wata waya don amfani da Datar wayar wani ko shi ya yi amfani da ta ka wayar, ( Wi-Fi Hotspots), haka zalika, ku guji shiga duk wani link na website da aka turo muku ta WhatsApp, Facebook ko Email da sunan cewa, in kuka shiga za ku samu wata garabasa, hakan zai taimaka gaya wajen yaki da tsagerun Internet.
Bugu da kari, sak**akon yadda lamarin kutsen yayi yawa jama'a da dama na kokawa kan yadda ake samun bayanansu na sirri, har a yada su. Munin lamarin shi ya sanya jama'a s**a fara neman mafita, har s**a fara daukar matakan da na lissafa su a baya.
Amma fa wannan ba yana nufin jama'a gaba daya ne suke daukar matakan ba, akwai wasu wadanda har yanzu sun yi kunnen uwar shegu shi ya sa suke ta fadawa tarkon tsagerun Internet da ke kutse wa jama'a a kafafen sada zumunta na zamani.
A mukalar yau, zan yi bayani ne dalla-dalla kan muhimmin matakin da za ku dauka don kare Facebook account din ku daga harin masu kutsen Internet (Hackers). Wannan muhimmiyar hanyar da za ku bi don kare Facebook account din ku kuwa, ita ce, kuyi tsarin da ake cewa, "Two Factor Authentication" da turanci.
Wato shi wannan tsari na Two Factor Authentication, wani tsari ne da ba wai kawai lambobin sirri (password), kake bukata ba don shiga Facebook account din-ka, a,a, sai an maka wani gwajin na daban, kafin a tabbatar da cewa, kaine wanda ka mallaki Facebook account din. Yadda lamarin ke faruwa kuwa shine; bayan ka kammala matakin saka lambar sirri (password), website na Facebook zai turomaka da sako dauke da wasu lambobi da ake cewa OTP ta email din-ka ko lambar wayarka, idan ka saka lambobin da aka turomakan ne to shikenan sai a amince maka ka shiga Facebook account din-ka. Wannan na nuna cewa, ko da mutum ya samu lambobin sirrinka (Password) da sunanka (Username), ta wata hanyar ba zai iya shiga ko kwace maka Facebook account din-ka ba.
Abin sha'awar ita ce, saita wannan tsari na Two Factor Authentication yana da matukar sauki, babu wahala ko kadan.
Yadda za ka saita shi kuwa shine k**ar haka: Da farko za ka shiga bangaren tsaro wato security na Facebook account din-ka ko Fejinka, sai kuma ka shiga sashen saiti wato Setting.
Za ka ma iya kallon yadda ake saitawa ta cikin wannan faifan bidiyo...
Haka kuma yana da kyau a koyawa jama'a yadda za su kaucewa wasu hanyoyin fadawa tarkon tsagerun Internet masu kutse. Alal misali, idan kai mutum ne mai ta'adar nan ta amfani da lambar sirri (Password) guda daya a dukkannin shafukan ka/account din-ka, mai kutsen Internet zai iya samun damar kwace maka su gaba daya idan ya samu lambar sirrinka (Password). Don kaucewa fadawa tarkon masu kutse, abin da za ka yi shine; ka guji amfani da lambar sirrinka (Password), iri daya a dukkannin shafuka/account din ka, ka kasance mai amfani da lambobin sirri wato Password kala-kala. Sannan lambobin kar su kasance masu saukin fahimta. Har Ila yau, ya k**ata kai mai amfani da kafar sada zumunta na zamani/soshiyal midiya ka kwana da sanin cewa, yin "Two Factor Authentication" wajibi ne gare-ka, ba wai zabi bane. Wani hanzari ba gudu ba, ya k**ata kusan cewa, yayin da yin"Two Factor Authentication" ya zama sahihiyar hanyar bai wa Facebook account da sauran shafukan sada zumunta na zamani kariya daga sharrin masu kutsen Internet, a bangare guda zai iya kasancewa babbar barazana ga mutumin da bai san yadda zai yi amfani da shi ba. Misali, masu kutsen Internet za su iya amfani da wata fasaha ake cewa "social engineering" inda za su yaudari mutum ya turo musu da cikakkun bayanansa na sirri, musamman lambobin OTP.
Yana da matukar muhimmanci kusan cewa kuskure ne babba, ku bai wa wani lambobin OTP da aka turo muku.
Daga karshe, idan har lambobin OTP dinka ana turo maka su ne ta lambar wayarka, to wajibi ne ka kula da layinka/sim card dinka sosai, domin in ka rasa shi, dai-dai ya ke da ka rasa Facebook account din-ka, sai dai in kana da wani tsari na biyu wato kayi amfani da email din-ka a matsayin jiran ko ta kwana.