14/04/2022
SHARSHI Ma’ana, halal a bayyane yake a cikin Alkur’ani da hadisai tabbatattu daga Annabi (S.A.W), haka kuma haramun a bayyane take a cikin Alkur’ani da hadisai tabbatattu daga Annabi (S.A.W), amma a tsakanin halal da haram, akwai wadansu al’amura masu rikitarwa; su ba su da sifa ta halal tsantsa, ballantana mu sa su a layin halal, bas u da siffa ta haram tsanrsa, ballantana mu sa su a layin haram. Don haka sai s**a zamanto masu k**a da juna, ko masu rikitarwa, ta yadda ba ka san ajin da za ka ajiye su ba. Wadannan abubuwa masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane ba su san su bu, ba su san hukuncinsu ba. Wannan yana nuna akwai wadansu kadan cikin munate sun san su, su ne malamai tabbattu a cikin ilimi, su bas u da rikici a cikin abin, da sun ga su kasa gane wane ayi ya k**ata su ba su. {Duba; Jami’ul Ulum wal Hikam Na Ibnu Rajab 1/181}. A nan wurin abin da malamai suke cewa shi ne, akwai abubuwan da dama da asalinsu ana daukar su a halal ne, ba ka da dammar ka cire su daga halacci, said a nassi, akwai kuma abubuwan da ake daukar su a matsayin haramci, ba ka da dammar ka cire su daga haramci, sai da nassi, k**ar misalign duk wani dangin abinci wanda zai karbi sunan addayyib, wanda kuma bincike ya nuna ba ya cutar da tunani, ba ya gurbata masa tunani, to wannan abin halal ne . idan ka bad a fatawa a kan halaccinsa, ba a abin ka bashin dalili, duk wanda ya bi ka bashin dalili, bai san abin da yake ba. Amma in wani ya zo ya yi da’awar haramci kana abin da yake yana cikin Addayyibat, to wanda ya yi da’awar haramcin, shi ne za’a ce ina dalilinsa? Saboda haka, asali dangane da abinci ko abin sha, matukar ya zama baya cutar da jiki, ko hankali to ya zama dayyib, shi kuma halal ne, Allah ya ce: ( ﻗﻞ ﺃﺣﻞ ﻟﻜﻢ ﺍﻟﻄﻴﺒﺖ ( )ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ4 : ) (Ka ce an halatta muku dukkan dangin abinci ko abin sha wanda yake daddada) Asali kuma cikin dukkan abinci ko abin shha wanda zai cutar da hankali, ko zai cutar da lakar jiki, yana shiga cikin babin haramun, idan ka ba fatawa da haramcinsa👉cigaba ☝