Allah Daya Gari Ban - Ban

Allah Daya Gari Ban - Ban

Share

Domin Ilimintar da MALAM BAHAUSHE akan wasu dabi'u na sauran kasashe. Allah yaimana jagora (AMEEN)

Auwalancy4us AIA

Ankirkiri wannan shafine domin zakulo wasu kyawawan Dabi'u da al'adu na wasu kasashen domin fadakar da al'ummar HAUSA domin dai agudu tare kuma atsira tare. Fatan mudai ace malam BAHAUSHE yasan kansa kuma ya yarda cewa shi mutum ne mai kima da kuma daraja a idanun DUNIYA!

02/04/2025

DUNIYA TSOHON GARI

Sadiq Tukur Gwarzo

Alkur’ani mai tsarki ya bayar da labarin mutanen ‘Ād (Adawa), wata tsohuwar al’umma da ta kasance mafi ƙarfi da ɗaukaka wadda ba a taɓa ganin irinta ba a duniya.
Labarinsu ya ja hankalin malamai, masana tarihi, da masu binciken ƙasa tsawon ƙarnoni. An siffanta su a matsayin al'umma masu girman jiki da s**a ƙi bin umarnin Allah, daga ƙarshe Allah ya shafe su daga tarihi, abin da ya sa labarinsu ya kasance darasi ga sauran al'umma.
A cikin ayoyi da dama, Alkur’ani ya bayyana ƙarfinsu. Allah ya aiko Annabi Hūd (A.S) don ya shiryar da su, amma s**a ƙi karɓar saƙonsa, s**a yi girman kai, sannan s**a ci gaba da zalunci da almubazzaranci.
Allah ya siffanta su da cewa ba a taɓa yin irinsu ba:
"Shin, ba ka gani yadda Ubangijinka Ya yi wa ‘Ād—[na] Iram, birnin da ke da manyan ginshiƙai, wanda ba a taɓa yin irinsa ba a duniya?" (Alkur’ani 89:6-8)
Malamai irin su Ibn Kathir sun bayyana cewa ‘Ādawa mutane ne masu tsayi da ƙarfi, kuma sun ƙware wajen gine-gine. Wasu ruwayoyi sun ce suna da tsayi har zuwa kimanin ƙafa 90 (ninkin tsawon mutanen yanzu sau 15). An ce sun gina manyan gine-gine masu haske da ƙawa da ababen alatu, wanda birninsu Iram ya ƙunshi tsararrun ginshiƙai da hasumiyoyi masu girma.
Malamai da dama sun bayyana girma da kuma halakar da ta faru ga ‘Ādawa.
Ibn Kathir, a cikin littafinsa Qasas al-Anbiya, ya bayyana cewa mutane ne da s**a fi sauran al’ummomi ƙarfi kuma sun gina manyan birane. Ya kawo ruwayoyi da ke cewa tsayinsu ya kai har cubit sittin (kimanin ƙafa 90). Amma saboda girman kai da rashin godiya, Allah ya aiko musu da wata iska mai azaba har tsawon darare bakwai da kwanaki takwas har sai da s**a rushe (Alkur’ani 69:6-7).
Imam Al-Tabari, a cikin tafsirinsa, ya bayyana cewa mutanen ‘Ādawa sun kware a gine-gine kuma sun gina manyan gine-gine da s**a fi kowane zamani girma. Ya kuma ambato ruwayoyi da ke nuna cewa an binne ragowar gine-ginensu a cikin hamadar Larabawa.
Gaskiyar Kimiyya da Binciken Tarihi
A cikin shekarar 1992, masana tarihi sun yi amfani da hotunan tauraron dan adam da tsoffin taswirori domin gano wani birni a cikin hamadar Rub' al Khali a Oman, wanda ake kira Ubar, ko kuma Iram Mai Ginshiƙai. Bincike ya nuna cewa birni ne da ya bunƙasa a cinikayya kafin ambaliyar yashi ta binne shi.
A cikin watan Maris na shekarar 2025 ne masu bincike Corrado Malanga na Jamiar Pisa, ta ƙasar Italy da Filippo Biondi na jamiar Strathclyde ta ƙasar Scotland, da sauransu s**a fitar da rahoton binciken wasu manyan hasumiyoyi da hasken SAR ya hango a ƙarƙashin dalar Giza na ƙasar Misira wanda kan iya sauya ɗaukacin tarihin da aka jima ana bayarwa game da Misira, a cewarsu tsayin hasumiyoyin guda takwas sun kai kimainin ƙafa 600, kuma sune ke ɗauke da dalar duwatsun Giza, abinda ya sanya mamaki a zukatan mutane musamman game da yadda mutanen da s**a rayu kimanin shekaru dubu uku zasu mallaki fasahar aiwatar da waɗannan gine-gine.
A zance mafi inganci, daga al'ummar Adawa da ake hasashen sun rayu a inda ƙasar Oman take a halin yanzu, zamu iya fahimtar cewa mutanen da s**a rayu gabanninmu sun mallaki fasahohin gine-gine da ƙere-ƙere waɗanda har yanzu ba a kai ga riskar kwatan-kwacinsu ba, sannan da yawansu sunyi fito na fito da Allah, don haka Allah ya halakar dasu tare da shafe tarihinsu a bayan ƙasa.
Tabbas, babu wani ƙarfi daya kusanci ƙarfin Allah. Kuma dukkan mai rai mamaci ne, amma Allah Ta'ala rayayye ne kuma wanzajje.

22/02/2025

SOJA DA SOJA: MANYAN DARUSSAN DAKE CIKIN LITTAFIN 'A JOURNEY IN SERVICE' NA TSOHON SHUGABAN ƘASA IBRAHIM B. BAGANGIDA

SADIQ TUKUR GWARZO

Littafin 'A Journey in Service' ya faro ne da tarihin rayuwa da aikin Janar Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya. Littafin yayi bayanin gwagwarmayar rayuwarsa tun daga ƙuruciyarsa a Minna da Wushishi, zuwa lokacin da ya fara aikin soja, har zuwa yadda ya zama ɗaya daga cikin muhimman shugabanni a harkokin mulkin Najeriya. Babangida ya yi nazari kan rawar da ya taka a lokutan da s**a kasance masu muhimmanci a tarihin Najeriya, ciki har da aiwatar da gyaran tattalin arziki, da ƙirƙirar sababbin jihohi, da kuma ƙoƙarin mayar da Najeriya zuwa mulkin farar hula, wanda aka fi tunawa da soke zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni, 1993.
Har ila yau, littafin ya shiga cikin rayuwarsa ta sirri, ilimin sojarsa, da kuma dangantakar da ta tsara aikinsa, tare da tunanin rayuwarsa ta bayan murabus musamman kan haɗin kai da da hidimtawa ƙasa.
Manyan Darussa Masu Muhimmanci daga cikin littafin

1. Kaɗaitakar Jagorori: Farashin Shugabanci
Labarin Babangida ya bayyana yadda ƙarfin iko, duk da cewa yana ba da izini da tasiri, yake kuma haifar da kaɗaici. A matsayin shugaban mulkin soja na Najeriya, Babangida ya yɗtsinci kansa a yanayin daya nesanta shi daga abokanansa, musamman bayan yanke shawarwari masu rikitarwa k**ar misalin aiwatar da shirye-shiryen daidaita tattalin arziki da soke zaɓen shugaban ƙasa na 1993.

Muhimmin Darasi:
Shugabanni sau da yawa suna tsintar kawunansu cikin kaɗaici a yayin da suke mulki, musamman lokacin da s**a yanke shawarar da ba mabiyansu ba su so ba. Gaskiyar shugabanci wani lokaci tana buƙatar sadaukar da alaƙar ƙashin kai don abin da ake ganin shine mafi alheri ga ƙasa.

2. Cin Amana Daga Masu Amana: Raunin Aminci
A duk tsawon aikinsa, Babangida ya fuskanci cin amana daga wadanda s**a fi kusa da shi – abokai na gari da abokanan aiki – waɗanda s**a bar shi a lokutan matsin lamba na siyasa, ko s**a yi ƙoƙarin raunana ikonsa don amfanin kansu. Daga cikin misalai akwai yadda ya cire gwamnatin Muhammadu Buhari a 1985, alhali a baya yayi matuƙar tallafa mata, hakan yana nuna yadda dangantakar siyasa ke iya sauyawa saboda bambancin hangen nesa.

Muhimmin Darasi:
Aminci a siyasa da shugabanci yakan dogara ne da yanayi. Waɗanda s**a fi kusa da shugaba na iya zama barazanar da ta fi tsanani idan burin kansu ya saɓawa burin jama'a.
3. Nauyin Rashin cika alƙawari: Soke Zaɓen 12 ga Yuni (June 12)

Soke zaɓen shugaban ƙasa na 1993 ya kasance muhimmin lokaci a shugabancin Babangida. Ya yi alkawarin miƙa mulki zuwa ga farar hula amma daga ƙarshe ya soke zaɓen da Moshood Abiola ya yi nasara a kai. Wannan matakin ya janyo rikici da zarge-zargen cin amana ga burin dimokiraɗiyyar Najeriya.

Muhimmin Darasi:
Cin amanar jama'a tana da sak**ako mai ɗorewa. Hasashen cin amana yana wuce lokacin mulkin shugaba, hakan kuma ke bayyana yadda tarihi zai tuna da wannan shugaban.

4. Iko Kamar Wuka ce mai baki biyu Biyu: Mulki da kuma Nauyin shugabanci
Gyare-gyaren Babangida, ciki har da haɗin gwiwarsa da IMF da aiwatar da Shirye-shiryen Daidaita Tattalin Arziki (SAP), sun kasance da kyakkyawar niyya don gyara lamurran tattalin arzikin Najeriya. Duk da haka, waɗannan gyare-gyare sun haifar da wahala ga yawancin 'yan Najeriya kuma an ɗauka cewa matakan suna amfanar da 'yan ƙalilan masu iko ne kaɗai.

Muhimmin Darasi:*
Shugabanci yana ɗauke da nauyin yanke shawarwari masu wuya musamman wajen tabbatar da cewa mafi yawan mabiya ne suke amfanuwa daga shawarwarin. Sai dai Rashin daidaitawa a wannan bangare na iya haifar da zarge-zargen son kai ko zalunci ga wannan shugaban.
5. Damalmala Tsarin Iko: Bayar da Kulawa ga ruwayoyin siyasa
Ɗaya daga cikin matakai masu cike da rikici da Babangida ya ɗauka shi ne ƙirƙirar jam'iyyun siyasa guda biyu da gwamnati ta tallafa wa wato 'National Republican Convention (NRC) da Social Democratic Party (SDP), da nufin kafa tsarin jam'iyyu biyu. Duk da cewa an ƙirƙiri tsarin ne don tallafawa tsarin dimokiraɗiyya, amma kuma masu s**ar lamari sun ɗauki wannan a matsayin hanyar tarnaƙi ga tafarkin siyasa tare da jange aukuwar samun sahihiyar adawa.

Muhimmin Darasi:
Shigar da ƙarfin iko ta hanyar tsarin siyasa da yadda ake sarrafa tsarin zai iya haifar da matsala, hakan yana janyo zarge-zargen mulkin k**a karya. Gaskiyar shugabanci tana buƙatar bayar da dama ga abokan adawa da kuma karfafa gasa ga ƴan siyasa domin samun nasarar mai gaskiya.

6. Gado Ya Fi Tsawon Lokacin Mulki: Kowanne Mulki yana da iyaka

Murabus ɗin Babangida a 1993, bayan matsin lamba na siyasa, ya nuna muhimmin darasi: duk kuwa da iko da shugaba ke da shi, lokacinsa a ofis na ɗan lokaci ne. Duk da haka, shawarar da ya yanke – ko ta zama mai kyau ko akasin haka – itace ke fayyace yadda tarihi zai tinƙa tunawa da shi.

Muhimmin Darasi:
Tasirin tafarkin shugabanci baya dogara ne akan tsawon lokacin da shugaba yayi a mulki , amma yana dogara akan gaskiyar ayyukansa da tasirin da za su yi wa makomar ƙasa a dogon lokaci.

7. Haɗin Kan Ƙasa da Bukatun Yankuna: Daidaito da Juna

A tsawon mulkinsa, Babangida ya yi ƙoƙari don tabbatar da haɗin kan Najeriya duk da ƙalubalen yankuna da bambancin kabila. Ƙirƙirar sababbin jihohi 13 a ƙarƙashin jagorancinsa an yi ne da nufin tallafawa haɗin kai, amma wasu sun fassara hakan a matsayin hanyar ƙarfafa iko na siyasa.
Muhimmin Darasi:
Haɗin kan ƙasa yana buƙatar daidaituwa tsakanin bai wa kabilu da yankuna dama da kuma kaucewa taruwar muƙaman iko a ɓangare ɗaya, wanda hakan zai iya ware wasu yankuna ko kabilu.

08/10/2024

SHIN INA LABARIN MAKOMAR WAƊANDA S**A GABACE MU?

SADIQ TUKUR GWARZO

Gabatarwa
Littafi mai tsarki Al Qur'ani, ya bayar da gamsasshen bayani game da makomar dukkan ɗan adam, musamman domin amsa tambayar da yawa-yawan mutane suke da ita a cikin zukatansu game da makomar mutanen da s**a gabace mu, domin hakan shine zai sa mai karatu yaji inda zai kasance bayan kammala wannan rayuwar ta duniya. A wannan muƙala, zamu kalli wasu ayoyin Alqur'ani tare da zantukan da kimiyya ya tabbatar zuwa yau domin gano inda mutanen da s**a gabace mu suke a yanzu.

*Surat Al-Baqarah (2:260)*
"Kuma lokacin da Ibrahima ya cewa Ubangijinsa 'Ya Ubangijina, ka nuna mini yadda kake rayar da matattu. Sai Ubangiji yace, 'shin baka yi imani bane?' sai yace, Nayi imani, amma [na tambaya ne] domin samun nutsuwar zuciya. Sai Allah Ta'ala yace "Ka ɗauki tsuntsaye guda huɗu, ka sanyasu kusa dakai, ka yayyankasu izuwa ƙananu. Ka rarraba (naman) su izuwa saman duwatsu, sannan ka kira su zuwa gare ka. Zasu zo da hanzari. Kayi sani cewa Haƙiƙa Allah mai girma ne kuma Buwayayye " (Quran 2:260)

A wannan Ayar, Annabi Ibrahim A.S ya nemi gamsar da zuciyarsa daga Ubangijinsa mai girma da ɗaukaka game da yadda Ubangiji zai tayar da matattu bayan an binne su a ƙaburbura, tsoka da ƙasusuwansu duk sun ruɓe. Sai kuwa Allah Ta'ala ya nuna masa cewa umarni kaɗai zai bayar wajen sake rayar da matattu.
Surat Hajj 22:5-6
Ya ku mutãne! Idan kun kasance a cikin shakka ( a game da) Tãshin ƙiyãma, to, lalle ne Mũ, Mun halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudãjin jini, sa'an nan kuma daga tsõka, wata ta kammala halittuwa da wata bata kammala halittuwa ba, dõmin Mu bayyana muku. Kuma Muka tabbatar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani lokaci ƙayyadajje, sa'an nan kuma Mukã fitar da ku (daga mahaifar) kunã jãrĩrai, sa'an nan kuma (muka sarrafa girman jikin ku) har ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa (tun da ƙuruciya), kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin rãyuwa (tsufan jiki) dõmin kada ya san kõme a bãyan ya sani. Kuma kunã ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kõwane nau'i mai ban sha'awa.
Haka nan ne ke faruwa dõmin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake rãyar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikone a kan kõme.
*Surat Ta-Ha (20:51)*

IKON ALLAH WAJEN RAYAR DA MATATTU
Dukkan waɗannan ayoyi sun yi nuni da ikon Allah wajen rayar da matattu da buƙatar imani da haka ga dukkanin musulmi.

HUJJOJIN KIMIYYA GAME DA RAYAR DA MUTUMIN DA YA MUTU
Duk da cewa kimiyya ba zata iya bayanin ikon Allah game da abinda ya ƙudurta ba musamman dangane da rayuwa da mutuwa, amma sak**akon binciken baya-bayan nan sun gaskata faɗinsa maɗaukakin sarki game da rayar da matattu.
Ga wasu daga hujjojin;-
1. *Cellular Regeneration*:
Masana kimiyya sun gano cewa akwai wasu halittu da suke rayar da wasu sassan jikkunansu bayan sun daina aiki ko sun mutu, misali hannaye da ƙafafu da sauransu. Misalinsu shine Salamandar da wasu dangin kifaye da ƙadangaru da sauransu.

2. DNA Preservation:
Zuzzurfan binciken da aka gudanar game da ƙwayoyin halittar ɗan Adam ya nuna cewa waɗannan ƙwayoyi masu ɗauke da ɗaukacin bayanai gami da sirrin halittar ɗan Adam watau DNA suna iya shafe dubunnan shekaru ba tare da sun lalace ba koda kuwa ƙasusuwa da tsokar ɗan adam ta ruɓe ko ta zama turɓaya. Wannan ke tabbatar da faɗin Allah Ta'ala cewa da Umarninsa kaɗai DNA zai iya ƙara samar da ɗaukacin jikin ɗan adam k**ar yadda ya rayu bayan gushewarsa da shekaru masu tarin yawa.

3. Fossil Record:
Ilimin kimiyyar ɓaraguzai yana bin diddigin tsohuwar rayuwar ɗan adam daga ɓurɓushin abinda yayi saura na jikinsa bayan tsawon lokaci da mutuwarsa. Da irin wannan ilimin ne kimiyya ta samu nasarar samar da siffofi da fuskokin mutanen da s**a gabata shekaru aru-aru da s**a shuɗe, ciki har da fuskar Fir'auna Seti II da ake hasashen yayi zamani da Annabi Musa A.S.
Tabbas, Ko daga nan za a iya gane cewa abune mafi sauƙi ga Allah Ta'ala ya rayar da matacce.

4. Neuroplasticity:
Binciken kimiyya a wannan fannin ya tabbatar da wani yanayi wanda yake kawwame zahiriyyar ɗan adam (abinda ya shafi tunani da ɗaukacin abinda ya sani) a wani waje na daban cikin maɗaukakiyar duniya bayan mutuwarsa anan duniya.

*AMSAR TAMBAYA: SHIN INA WAƊANDA S**A GABACE MU SUKE?*
Kamar yadda aka gani, Allah Ta'ala ya faɗa a wurare mabanbanta cikin littafinsa mai tsarki Alqur'ani cewa shine ya halitta ɗan adam kuma shine zai sake rayar dashi bayan mutuwarsa, don haka sai gashi binciken kimiyyar zamani ya tabbatar da wannan iko na Allah Ta'ala game da sake rayar da ɗan adam koda kuwa gangar jikinsa ta ruɓe, sannan kuma zai sake dawo masa da tunaninsa da ruhinsa a duk sanda yaso..
Abubuwan Lura:
1. Idan mutum ya mutu, ruhinsa na tashi zuwa sama, amma bayan lokaci kaɗan sai ya dawo domin amsa tambayoyi. Amsa waɗannan tambayoyin shine zai yi nuni da makomar ruhin ta gaba.
Daga abinda ya inganta na ilimi, Wanda duk ya aikata kyawawan ayyuka, Ruhinsa zai kasance a kyakkyawar makoma, yayinda wanda ya aikata akasin haka Ruhinsa zai kasance a mummunar makoma. A waɗannan wurare ruhi zai yi zaman saurare har zuwa ranar Hisabi.
2. Allah zai sake rayar da gangar jikin mutanen da s**a gabata duk da yake sun rayu a wannan duniyar har kuma an binnesu, sannan da yawa ana iya cewa ɗaukacin jikin ya zagwanye, ya ruɓe har ma ya zama turɓaya.
3. Allah zai mayarwa da mutum zahiriyyarsa k**ar yadda yake alkintata bayan ya rasu, don haka babu shakka dukkan ɗan adam zai mutu, kuma Allah zai rayar da dukkan matacce, sai kuma ya yi masa hisabin abinda ya aikata a wannan rayuwar ta duniya.
(SUBHANAKA UJBUN LIMAY YA'ARIFUKA)
HUJJAR KIMIYYA MAI TABBATAR DA ƊAN ADAM YANA SAKE MOTSI BAYAN YA MUTU
Wani sabon bincike da gungun masana ƙarƙashin Alyson Wilson — na Central Queensland University dake Rockhampton, a ƙasar Australia ya tabbatar da cewa gawar ɗan adam na motsi, har ma takan iya shiga cikin masifa bayan mutuwa.
Masanan sun lura da cewa wasu gawarwakin kan canza fuskar kwanciya saɓanin wadda aka sanyasu cikin kabari da ita, wasu kuma kan sauya zuwa mummunan yanayi jim kaɗan da binnewa.. manufar binciken shine gano yadda gawar ɗan adam ke ruɓewa ko rashin ruɓewa bayan binnewa a kabari.
Tabbas, wannan lokaci yafi k**a da lokacin amsa rambayar kabari!
*Madogarar bincike*
- Tafseer Ibn Kathir
- Tarjamar Al-qur'ani da Hausa
- Scientific journals and publications (e.g., Nature, Science)
- Online resources and documentaries on cellular regeneration, DNA preservation, and quantum biology.
-Medicalnewstoday

05/10/2024

MANYAN ABUBUWAN MAMAKI DA KIMIYYA TA TABBATAR GAME DA ISRA'I DA MI'IRAJI

Sadiq Tukur Gwarzo

A cikin ɗaukacin muhimman abubuwan da Annabi Muhammad s.a.w ya kawo game da addinin Islama, zancen tafiyar da aka taɓa yi dashi zuwa Qudus a wani dare da kuma ɗaukarsa zuwa Wurin Ubangijinsa 'Israi da Miiraji' na ɗaya daga cikin gagaruman lamurori waɗanda s**a ƙarawa wasu imani, yayinda wasu kuma s**a ƙara kafirci.
Wannan tafiya mai ban mamaki wadda bayananta yazo a littafi mai tsarki Alqur'ani da wasu ingantattun hadisai, ta saɓawa hankalin mutanen dake wancan zamani (sai dai waɗanda s**a gaskata fiyayyen halitta sunyi imani da gaskiyarsa, don haka s**a kore shakku a cikin lamarin), amma zuwa yanzu kimanin shekaru dubu da ɗari huɗu, kimiyya ta gaskata abubuwa da yawa game da wannan tafiya.
Yadda Labarin yake a taƙaice
A ranar 27 ga watan Rajab, kimanin watanni 6 kafin Hijira, cikin shekarar 621 CE, Malaika Jibril A.S yayi tafiya da Ma'aikin Allah Annabi Muhammad (s.a.w) akan Buraƙa daga birnin Makka zuwa birnin Qudus, inda ya limanci Annabawa masu daraja s**a gudanar da Sallah, daga nan kuma aka ɗauke shi izuwa sararin samaniya, aka keta sammai bakwai zuwa inda har yau tunanin ɗan adam bai kai ga riskarwa ba.
A wannan tafiya, an nunawa Annabin Allah ababen mamaki mabanbanta, tun daga Annabawan Allah da s**a gabace shi, zuwa yanayin sararin samaniya da taurari. Anyi tafiya dashi gaba da lokaci ta yadda yaga ƴan wuta da ƴan aljanna, sannan a wannan tafiyar ne kuma ya shiga fadar Allah Maɗaukakin Sarki ya karɓo Salloli biyar da aka wajabtawa dukkanin musulmai, inda har wasu Malaman s**a ce idanuwansa sun riski ganin Allah ƙuru-ƙuru. (Allah ne mafi sani)

*Abinda kimiyya ta samo*

Bisa nazartar wannan tafiya ta kafar binciken kimiyyar zamani, ga abubuwan da aka samo:-

1. Wormhole
A cikin shekarar 1935, masu binciken kimiyya Einstein da Nathan Rosen sunyi amfani da tunanin dai-daito da ake kira 'general relativity' wajen bayyana yiwuwar samun wata gada mai iya haɗa lokaci da tazara, wadda a taƙaice ana iya cewa tana iya rage nisa da lokacin riskar wurare masu nisan zango. Sunan da s**a sanyawa wannan gada shine 'wormhole'.
Masana da yawa sun gamsu da cewa akwai ƙadamin da za a iya tafiya zuwa wuri mai nisan zango cikin ƙanƙanin lokaci, don haka tafiyar da akayi da Annabin Allah Muhammad s.a.w tana da gurbi a kimiyance.

2. *Near-Death Experiences (NDEs)*:
Binciken kimiyyar da akeyi game da wani yanayi da ɗan adam ke shiga wanda ake kira da Hausa 'dogon suma' ya tabbatar da gaskatar wani yanayi wanda zai sa kimiyya ta karɓi tafiyar da akayi da Annabi Muhammad s.a.w daga duniya zuwa sararin samaniya.
Wannan yanayi ya haɗa abubuwa k**ar haka:-

- Fahimtar zahiriyyar ɗan adam daga wajen jiki (misalin fitar ruhi daga wajen jiki )
- Haɗuwa da waɗanda s**a taɓa rayuwa a duniya
- Shaida rayuwar bayan mutuwa
- Jin nutsuwa da aminci

3. *Consciousness Beyond the Brain*:
Duk da cewa akwai saɓani game da cewa shin da Ruhin ma'aikin Allah s.a.w akayi wannan tafiya ko da ɗaukacin jikinsa, amma dai binciken fannin kimiyyar kwakwalwa ya gano cewa zahiriyya na iya wanzuwa da karan-kanta a wani wuri daje nesa da ƙwaƙwalwar ɗan adam.
Sak**akon wani binciken baya-bayan nan ma da masani Dr. Michael Pravica ya gabatar yayi hasashen cewa zahiriyya na zuwa ne daga wata kusurwa ta maɗaukakiyar duniya (Universe), hakan na nufin maɗaukakiyar duniya na da kusurwowi sama da huɗu da akafi sani, watau akwai wasu kusurwowin bayan kusurwar tsayi da faɗinta, da tazararta da kuma lokacinta, don haka masana kimiyya sun fahimci cewa zahiriyya na iya fita daga gangar jiki har kuma tayi tafiya izuwa wasu sassan duniya sannan kuma ta dawo cikin jiki tare da labarta halayen data riska.

4. *The Speed of Light and Time Dilation*:
Tafiyar da akayi da Ma'aikin Allah Annabi Muhammad s.a.w zuwa sararin samaniya tare da keta manyan hijabai cikin ƙanƙanin lokaci ya yi dai-dai da tsarin kimiyya da yayi magana game da tazara gami da lokaci.
Tsarin kimiyya ya tabbatar da cewa akwai alaƙa tsakanin cin gagarumar tazarar tafiya cikin ƙanƙanin lokaci gwargwadon saurin abin hawa.
Anan duniya, babban ma'aunin lissafta tazarar sararin samaniya shine gudun hasken rana, don haka aka ƙadarta cewa da zarar an samar da na'urar da zata yi tafiya sama da saurin haske, to tabbas za a iya tafiya zuwa duniyoyin taurarin dake sararin samaniya, hakan kuwa dai-dai yake da yin tafiya gaba da lokaci.
Sabili da haka, kimiyya zata karɓi wannan tafiya bisa hujjar cewa an yita akan abin hawan da saurinsa ya kere na hasken rana da mamakon yawa.

Mahaɗar Kimiyya da Addini

Lamarin Isra' da-Mi'raj na nuni da wata mahaɗar dake tsakanin addini da kimiyya kasancewar lamarin ya kawo abubuwan da bayan shafe tsawon lokaci, kimiyya na bayar da bayani kwatan-kwacin yadda aka bayar a addinance.
Tafiyar na nuna mana cewa;-

- Akwai abubuwa zahirarru da s**a wanzu saɓanin waɗanda muka sani ko muke iya gani a wannan duniyar tamu.
- Cewa zahiriyyar ɗan adam na iya ketawa zuwa shingayen da bamu tsinkaya ba.
- Cewa addini da kimiyya na iya tallafar kowanne da hujjoji wajen ƙarfafa binciken ilimi.
(Allahumma Salli Ala Muhammad s.a.w)

Madogara:

- Quran (17:1, 53:4-18)
- Hadith collections (Bukhari, Muslim)
- "The Miraculous Journey of Prophet Muhammad" by Ibn Hisham
- "The Isra' wal-Mi'raj" by Al-Suyuti
- Scientific studies on wormholes, NDEs, quantum entanglement, consciousness, and time dilation.

04/09/2024

NAZARI GAME DA SAKE DAWOWAR RUHI RAYUWAR DUNIYA BAYAN MUTUWA

Sadiq Tukur Gwarzo
Kashi na Huɗu

MAHANGAR ADDININ ISLAMA

Dawowar Ruhi don sake rayuwa a wannan duniyar a jikin wani ɗan adam na daban bayan mutuwa abune da addinai daban-daban s**a bayar da bayanansu akai. Sai dai, a mafi ingancin zantuka, akwai mahawarori akan wannan lamari a addinin Islama, masanan da s**a Nazarci littafin Al Qur'ani mai tsarki da zantukan malamai sun yi tsokacin akwai buƙatar taka tsan-tsan da nazari wajen yanke hukunci game da batutuwan da s**a shafi goyon bayan dawowar Ruhi wannan duniyar bayan mutuwa.
Kai tsaye, malamai sun faɗi cewa littafin Alqur'ani bai ambaci maganar 'Reincarnation' dawowar Ruhi wannan duniyar ba. Abinda yawan-yawan Malumma s**a aminta dashi shine; akwai duniyoyin Rauhanai da Allah ya halitta kala-kala, daga ciki akwai sabbin Rauhanai da ake basu izinin shigowa cikin mahaifa a wannan duniyar da kuma duniyoyin Rauhanan da s**a kammala rayuwar duniya.
Don haka idan ɗan Adam ya rasu, to ruhinsa zai fita daga nan duniya zuwa ɗaya daga cikin duniyoyin Ruhanai guda biyu gwargwadon ayyukan da ya aikata, watau wanda ya aikata alheri ya tafi zuwa duniyar 'Illiyin' wanda kuma ya aikata mummuman aiki ruhinsa zai tafi zuwa 'Sijjiyn', anan waɗannan Rauhanai zasu cigaba da zama har zuwa ranar Hisabi.
Ga wasu Ayoyi da s**a yi maganar asali da makomar Ruhi k**ar haka;-

1. _Asalin Ruhi:_ "وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ مِن سُلَـٰلَةٍۢ مِّن طِينٍۢ ١٢ ثُمَّ جَعَلْنَـٰهُ نُطْفَةًۭ فِى قَرَارٍۢ مَّكِينٍۢ ١٣." (Quran 23:12-13)
- قَالَ رَبُّكَ لِلۡمَلٰۤـئِكَةِ اِنِّىۡ خَالـِقٌۢ بَشَرًا مِّنۡ صَلۡصَالٍ مِّنۡ حَمَاٍ مَّسۡنُوۡنٍ‏  فَاِذَا سَوَّيۡتُهٗ وَنَفَخۡتُ فِيۡهِ مِنۡ رُّوۡحِىۡ فَقَعُوۡا لَهٗ سٰجِدِيۡنَ‏(, 38:72
A taƙaice, Allah Ta'ala ya faɗa cewa shine wanda ya halicci mutum daga taɓo sannan ya hura masa Ruhi
2. _Lamarin Ruhi:
_وَيَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلرُّوحِ ۖ قُلِ ٱلرُّوحُ مِنْ أَمْرِ رَبِّى وَمَآ أُوتِيتُم مِّنَ ٱلْعِلْمِ إِلَّا قَلِيلًۭا ٨٥ (Quran 17:85)
A taƙaice Allah Ta'ala ya faɗa cewa Ruhi wani lamari ne daga gareshi, kuma mutane basu da sani a game dashi sai ɗan kaɗan.
3. _Makomar Ruhi:_ "كُلُّ نَفۡسٍ ذَآئِقَةُ الۡمَوۡتِ​ؕ وَاِنَّمَا تُوَفَّوۡنَ اُجُوۡرَكُمۡ يَوۡمَ الۡقِيٰمَةِ​ؕ فَمَنۡ زُحۡزِحَ عَنِ النَّارِ وَاُدۡخِلَ الۡجَـنَّةَ فَقَدۡ فَازَ ​ؕ وَمَا الۡحَيٰوةُ الدُّنۡيَاۤ اِلَّا مَتَاعُ الۡغُ." (Quran 3:185)
اِنَّ اِلٰى رَبِّكَ الرُّجۡعٰىؕ -QUR'AN 96:8
-QURAN 83:7كَلَّآ إِنَّ كِتَـٰبَ ٱلْفُجَّارِ لَفِى سِجِّينٍۢ ٧

كَلَّآ إِنَّ كِتَـٰبَ ٱلْأَبْرَارِ لَفِى عِلِّيِّينَ ١٨ Quran 83:18-
A taƙaice, Allah Ta'ala ya faɗa cewa Ruhi daga gareshi yake kuma gareshi zai koma, sannan za ayi masa Hisabin ayyukansa na nan duniya.

Ga abinda wasu manyan Malamai s**a zantar akan Ruhi:-

1. _Imam Ghazali:_ "Ruhi wani lamari ne na musamman da yake tsira bayan ɗan adam ya mutu, amma tafiyarsa bata dawowa (not reincarnation). Kawai dai sauyin rayuwa ake samu daga rayuwar duniya zuwa rayuwar lahira"
2. _Ibn Arabi:_ "Gundarin Ruhi baya sauyawa, amma yadda yake bayyana kan iya sauyawa tamkar yadda ruwa ke sauyawa daga lamirin ruwa-ruwa zuwa tururi amma duk da haka sunansa ruwa"
3. _Shaykh ibn Uthaymeen:_ "Babu zancen dawowar Ruhi don sake rayuwa a wannan duniyar a Musulunci, domin hakan yaci karo da Ayoyin Alqurani game da rayuwa guda ɗaya ga kowanne ɗan adam, da mutuwa da kuma hisabi"
Saboda haka, idan an lura za a ga cewa mafi yawan Malaman Addinin Islama basa goyon bayan dawowar Ruhi don sake rayuwa a jikin wani ɗan adam na daban bisa hujjar cewa hakan yaci karo da koyarwar addinin Islama game da lamarin tafiyar Ruhi da kuma Ranar Lahira.
(Madogarar Bincike:_
- Quran translations by Sahih International and Yusuf Ali
- Imam Ghazali's "The Book of the Soul"
- Ibn Arabi's "The Bezels of Wisdom"
- Shaykh ibn Uthaymeen's "Explanation of the Quran")
zamu cigaba insha Allahu

20/08/2024

TATTAKI BAYA DA LOKACI: LABARIN OMM SETI, MACEN DA TAYI IƘIRARIN TA RAYUI DA FIR'AUNAN MISIRA SETI (Shekaru 3,300 da s**a gabata)

SADIQ TUKUR GWARZO

A lokacin da ta fara ziyartar ƙasar Misira, tayi iƙirarin sabawa da wajen, amma tana iya yiwuwa rabonta da Misira ya kai kimanin shekaru 3000 da ɗoriya.

Dorothy Louise Eady shine cikakken sunanta, itace matar da tayi iƙararin cewa ta rayu da Firauna Seti na tsawon wasu shekaru kafin ta mutu a wancan lokacin, don haka ruhinta ne ya sake dawowa duniya a karo na biyu, abinda akafi ambata da suna 'REINCARNATION'.

Dorothy Eady, wadda ake yiwa laƙabi da “Omm Sety” ko “Om Seti” haifaffiyar ƙasar Ingila ce, an haifeta a kwanan wata 16 ga watan Janairun 1904. Ita mutum ce k**ar kowanne ɗan adam, har zuwa lokacin da wani haɗari ya same ta a shekarar 1907, tana da shekaru kenan da haihuwa.

Abinda ya faru shine, Wata rana Dorothy na gudu akan ƙafar bene sai ta zame ta faɗo ƙasa. Nan take ta suma. Iyayenta s**a kirawo likita domin ya duba lafiyarta, amma bai samu damar iya yin komai ba sai dai tabbatar musu da cewa yarinyarsu ta Rasu.

Ga mamakinsa, awa ɗaya da faruwar wannaan lamarin, koda ya komo gidan, ya shiga ɗakin daya bar gawar Dorothy, sai ya ganta ras da ita tana ta walwala.
Tun daga nan Dorothy ta soma yin mafarkai masu ban mamaki, inda ta kan hangi kanta a cikin gagarumin lambu, ko wata ƙasaitacciyar fada da mak**antansu.
Dorothy na da shekaru 4 da haihuwa aka kaita gidan tarihin Birtaniya. Koda shigar ta sashen tarihin ƙasar Misira, nan take ta soma tunano abubuwan da s**a faru da ita a rayuwarta ta baya.
Dorothy ta tabbatar da cewa an sake haihuwar ruhinta ne a kashi na biyu, sannan ta iya zayyano abubuwa da ta kiyaye sun faru a zamanin da take rayuwa a ƙasar Misira, asali ma tace tana ɗaya daga cikin matayen Fir'auna Seti.
Dorothy ta faɗi cewa sunan da ake kiranta a tsohuwar rayuwarta shine Bentreshyt, mahaifinta mai siyar da kayan marmari ne, kuma yana cikin dakarun birnin Abydos maintsarki. Ta rayu gami da bauta a fadar Fir'aunan Misira Seti.
Tun Dorothy na da shekaru 5 ta iya karanta duk wani abu da aka rubuta da yaren Hiragiliyanci mai tsananin wahala. A lokacin da ta cika shekara 10 da haihuwa tayi nasarar haɗuwa da Farfesa Sir Ernest Alfred Thompson Wallis Budge, babban masani a sashen Ilimin tsohuwar Misira, wanda yake aiki a gidan tarihin ƙasar Birtaniya.
Farfesa Ernest ya ɗau jimirin koyar da Dorothy tsohon harshen da Misirawan dauri suke amfani dashi, sai dai ya cika da mamaki yadda ya ga tana da ƙwarewa a fannin. Dorothy ta tabbatar da cewa ta san wannan harshe shekaru aru-aru da s**a gabata.
A cikin shekarar 1932, Dorothy ta bar ƙasar Ingila izuwa ƙasar Misira (Egypt), tana rayuwa da mijinta da ta aura mai suna Eman Abdel Meguid, wani ɗalibi da ta haɗu dashi a ƙasar Ingila.

Sa'ar da ta risƙi ƙasar Misira, sai ta durƙusa ƙasa ta sumbaci turɓaya, sannan tace ta dawo gida da zama.
Ance aurensu da mijinta Eman ya warware bayan shekaru biyu, amma sun samu ɗa da ta sanyawa suna Seti, asalin inda aka laƙaba mata 'Oum Seti' kenan.
A tsawon shekaru, Dorothy tayi bakin iyawarta wajen tunawa da abubuwan da s**a auku da ita a rayuwarta ta baya, dubunnan shekaru da s**a gabata.
Dorothy ta kiyaye cewa a rayuwarta ta baya, ana ambatonta da suna Bentreshyt, kuma tun tana da kimanin shekaru 3 da haihuwa aka kaita fadar birnin Abydos, anan ta rayu har ƙarshen rayuwarta. Ta ambaci cewa akwai wani aljani mai suna Hor-Ra, wanda yake yawan zuwa gareta, kuma shine yake taimakonta wajen warware sirrikan rayuwarta ta baya.
Mahaifinta ne ya kaita dadar Abydos wannan riƙo bayan rasuwar mahaifiyarta, saboda ya gaza ɗaukar ɗawainiyarta.

Bayan ta riski budurtaka ne ta haɗu da Fir'auna Seti I, har kuma s**a fara son juna, daga bisani ta ɗauki cikinsa, sai dai ƙarshen tarayyar bata zama mai faranta zuciya ba.
Dorothy ta shafe shekara ɗaya tana taimakon masu binciken kufan tsoffin fadojin Misira da muhimman bayanai, kuma mafi yawan bayanan da take bayarwa ingantattu ne.
Domin gaskata iƙirarin Dorothy na cewa ta taɓa rayuwa a Misira shekaru Tɗsama da dubunuku da s**a gabata, babban mai bincuken sashen Masarautar Seti ta taɓa yunƙurin aunata.
A lokacin tuhumar, an umarceta ta tsaya cikin duhu a gaban wasu zanukan bango, sannan aka nemi ta bada ba'asin abubuwan da zanukan ke nufi gwargwadon iliminta na tsohuwar rayuwar da ta taɓa yi a baya. Amsoshin da ta bayar sun baiwa kowa mamaki.
Abinda yafi ɗaurewa mutane kai shine, waɗannan zanuka da Dorathy ta fassara ma'anoninsu, babu wani mahaluki a duniya daya taɓa jimirin yin haka. Ana iya cewa ma babu wanda ya taɓa ganinsu sai a lokacin. Don haka ba kawai fassarar ma'anoninsu kaɗai tayi ba, sai da ta sanar da masanan abubuwan da basu kai ga ganowa ba.
Labarin Omm Seti ya shahara sosai. Ta taimaka wajen fassara lamurori masu wahalar gaske game da tarihin Misira ta dauri, iliminta ya taimakawa gungun masu bincike fahimtar manyar lamurori a fadar Abydos.
An taɓa tambayarta game da ƙabarin kyakkyawar Sarauniyar nan da ake hasashen ta taɓa hawa kan karagar mulkin Misira watau Nefertiti, mahaifiyar Fir'auna Tutankhamun, ga abinda take cewa k**ar yadda jaridar Washinton Post ta taɓa wallafawa a shafinta
“Na taɓa tambayar mai martaba (Firauna Seti) inda Kabarin yake, sai yace me yasa k**e son sani? sai nace masa saboda inaso a haƙo shi, sai yace "kada ki kusa kiyi haka". Lallai ya faɗa mini inda kabarin yake, kuma zan iya sanar daku inda yake. Yana can cikin kufen sarakuna kusa da kabarin Tutankhamun, a inda babu wanda zai iya tunaninsa" Tayi dariya sannan tace " kuma har yanzu babu abinda ya sameshi". .

Want your school to be the top-listed School/college in Ahmedabad?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Address

Ahmedabad
234