Tips on the Scholars interpretations on the term [ حسن صحيح] famously used by Al-Imam Attirmizy in His Sunan.
Recitation of the connected hadith chains to the famous Fourty hadith collection of Al-imam Annaway.
By Sayyid Ibrahim Niass Shuru
✍️ Page handlers
Durus Sayyid Ibrahim Niass shuru
هو كاتب وباحث في الحديث والأصول وسائر العلوم العقلية والنقلية، له عشرات الأبحاث في مختلف ميادين المعرفة
A logical intellectual islamic law
[ عدم صحة الدليل لا يدل على عدم صحة المدلول]
Vividly Explained By Sayyid Ibrahim Niass shuru
Page handlers ✍️
The pure lineage of Our beloved prophet Muhammad (S.A.W) from Sayyiduna Abdullah/Amina to Prophet Adam Alaihi salam
By Sayyid Ibrahim Niass shuru.
✍️Page handlers
.
📌Gabatarwa Ga📗 Littafin (2)
(ALLUMA') Fe Usulul Fiqhu (مقدمة الكتاب)
🎤 Sayyid Ibrahim Niass Shuru
17/04/2025
Assalamu Alaikum! 📢
---------------------
Saboda samun sauke karatukan sharhin littafin ( اللمع في أصول الفقه) da SAYYID IBRAHIM NIASS SHURU Ke gabatarwa a tsarin Audio🔊
za'a iya shiga wannan shafin na telegram.
👇👇
[https://t.me/durussyydnias]
--------------
📌Gabatarwa Ga📗 Littafin (1)
(ALLUMA') Usulul Fiqhu (مقدمة الكتاب)
🎤 Sayyid Ibrahim Niass Shuru
Isnadin littafin zuwa ga mawallafin sa.
SHINFIDA (3) AKAN ILIMIN USULUL FIQH
Daga Bakin: sayyid Ibrahim Niass shuru
*Taqaitaccen Nazari akan Rudewar da ake Samu tsakanin Mabahith Na Masana’antar Hadisi da fiqhu*
A cikin ilimin hadisi, akwai wasu babi da s**a fi k**a da fannin usulul-fiqh fiye da babobin Masana’antar hadisi, k**ar nasikh da mansukh, da aiki da hadisi mai rauni, da fiqhul hadith=wanda Al-Hakim ya ware masa babi a cikin Ma’arifatu ‘Ulumul-Hadith, da Mak**antan su.
Wannan Chakuďewar ta jawo Wadanda ba su da zurfi Cikin fahimtar Haðewar batutuwan biyu, har s**a riƙa yin hukunci da ilimin hadisi Cikin abubuwan da ba su dace dashi ba, sai dai a fagen usulul-fiqh da fiqhu!
Sabida haka Kasani cewa maudu’in ilimin hadisi shi ne sanin halayen matani da sanadodi domin a bambanta tsakanin ingantacce da mara inganci.
Imam Assuyuty Ya fada acikin Baitukan sa yana Cewa :
علم الحديث ذو قوانينِ تُحد
Ilimin hadisi yana da ƙa’idojin da s**a kayyade shi,
يدرى به أحوال متن وسند*
Wanda ake sanin halayen Matani da Sanadi dasu,
فذانك الموضوع والمقصود
Wadannan biyun - Süne Maudu’i , abin nufi 👇
أن يعرف المقبول والمردود
Shine asan (Almaqbul) Wanda Ake karba, Da (Al’Mardud) Wanda ake mayarwa.
Amma ingancin hadisi dön kafa hujja ko aiki ,
Wannan fage ne na usulii-fiqihii!
Shi muhaddisi yana gama aikinsa ne ta hanyar tantance hadisi, da bincikensa, da yin nazarinsa, da tace shi har sai ya san matsayinsa daga sahihanci ne ko rauni. Sannan sai ya gabatar da sak**akon bincikensa ga malaman fiqhu da usulul-fiqh, yana cewa: ‘Ga hadisin nan, sahihi ne a gare mu,’ ko kuma ya ce: ‘Ga hadisin nan, Me rauni ne a cikin sana’armu, ta hadisi, sannan sai ya bar su.
Daga nan, masanin usulul-fiqh yana kallon hadisin ne ta fuskar ma’anonin lafuzzansa don ya fahimci abin da yake nufi –Shin yana nuna wajibi ne ‘ Ko mustahabbi, Ko makaruhi, ko haramci. Sannan yana nazarin dalilan shari’a gaba ɗaya don tabbatar da ko akwai wani hadisi ko dalili da ke saba wa wannan hadisin. Idan ya samu hakan, sai ya fara aiki da ka’idojin warware sabani da fifiko (tarjih).…..har sai ya kai ga yanke hukuncin cewa hadisin yana da ingancin da za a iya aiki da shi.
Wannan yana shafan hadisi duka, ko sahihi ne ko kuma me rauni. Domin ana yin aiki da hadisin da ya samu raunuka a cikin hukunce-hukuncen shari’a da kyawawan ayyuka (فضائل الأعمال)
muddin ba shi da matuƙar rauni, ko baƙon rauni ، ko kuma ƙirƙirarre (mawḍū i), bisa yarjejeniyar manyan masana hadisi, fakihai, da malaman usulul-fiqh. Kuma ana yin hakan ne bisa sharuddan da aka ambata a muhalinsu . Wannan kuwa ya zama ijtihadin da manyan malaman mazhaba hudu, da sauran manyan masana s**a yi aiki da shi. Amma ba a nan ne wurin bayani dalla-dalla ba.”
Saboda haka, zaka ga wani hadisi ingantacce a cikin Sahihul Bukhari k**ar hadisin (إنما الماء من الماء)
amma yawancin malamai ba su yi aiki da shi ba, duk da ingancinsa, amma yana da wani hadisi dake Sabani dashi.
Kuma zaka ga wani hadisi mai rauni a cikin Sunan Tirmizi k**ar hadisin (هو الطهور ماؤه الحل ميتته), amma malamai sun yi aiki da shi.
Sabida haka ne, Nayi mamakin hazakar Imam Tirmizi wajen sanya wa littafinsa suna👇
«الجامع المختصر من السنن ومعرفة الصحيح والمعلول وما عليه العمل»
Acikin sa , Ya haɗa da fagen ilimin hadisi da ilimin fiqhu, Sabida hakane, al-Hafiz Abdullah as-Siddiq Al،Ghumari ya fifita cewa ɗalibi ya fi mai da hankali akan Sunan Na imam Tirmizi kafin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim, domin zai koyi fannonin hadisi da fiqhu a lokaci guda.”
Adadin hadisan dasuke cikin Sunan Tirmizi su ne (3956) A cikinsa akwai sahihai, hasanai, da raunana. Tare da haka Imam tirmizi yana fada acikin (ilal) (littafin da ke bayanin kurakurai da lahani na hadisi) Yana cewa: Dukkan abinda da ke cikin wannan littafi –Na Hadisi – sahihai ne, Ko hasanai, ko raunana, to ana aiki da su, Hakika wasu daga cikin malamai sun karɓe su, sai dai hadisi biyu kacal.
Sai ya ambace su (wato hadisan da ba a yi aiki da su ba)
Duk da cewa *Ibn Rajab al-Hanbali* ya yi sabani da shi a kan waɗannan hadisai biyun” acikin littafin sa : «شرح العلل»
Da kuma *Al-hafeez Ahmad Al-gumari* acikin littafin sa :
«المَثْنَونِي والبَتَّار»
sun soki wannan maganar, inda s**a ce har waɗancan hadisai biyun ma ana aiki da su.
Na’aam….Wannan baya nufin hana aiki da ilimin hadisi ko ƙuntata masa , domin ilimin yana da yalwa kuma yana da faɗi. Haka nan, muhaddisi na iya kasancewa Masanin fiqhu da usulul-fiqhi a lokaci guda, wanda hakan shine abin da ake buƙata. shine dalilin da yasa
*Al-Khadibul-Baghdadi* ya wallafa littafinsa :
«الفقيه والمتفقه»
A maimakon haka shi ne dalilin da yasa…(*Arraamahur’muzeey*)
Ya Wallafa littafin sa
«المحدث الفاصل بين الراوي والواعي»
Wannan shine asalinsa kafin a fara Rubuce-rubuce da rarrabe fannonin ilimi daban-daban. Don haka, duk wanda ya haɗa ilimin hadisi da fiqhu, Hakika Yazama Muhaqqiq.
ya cimma abin da ake Bukata .
Sheikh Ibrahim Inyass Shuru …
Fassara…….✍️
Ibrahim S Kawuwa
خليل الله الأزهري
*نظرة عابرة على الخلط بين مباحث الصناعة الحديثية والفقهية* |
فى علوم الحديث أبواب هي أشبه بأبواب الأصول منها إلى أبواب الصناعة الحديثية كباب الناسخ والمنسوخ والعمل بالحديث الضعيف وفقه الحديث =الذي تفرد الحاكم بالتبويب له فى معرفة علوم الحديث = وغير ذلك: وهذا التداخل جرَّ غير مدقِّقٍ الى الخلط بين الصناعتين فيحتكم إلى علم الحديث فيما لا يقضي فيه الا علم الأصول والفقه!
فاعلم أنَّ موضوع علم الحديث «دراية أحوال المتون والأسانيد للمعرفة والتعريف بصحيح الحديث من سقيمه» قال السيوطي:
علم الحديث ذو قوانين تحد
يدرى به أحوال مـتن وسنــد
فذانك الموضوع والمقصــود
أن يعرف المقــبول والمردود
أما صلاحية الحديث للاحتجاج والعمل فعمل أصوليٌ فقهيٌ!!! فكلَّما وجدتَ محدثا يتحدث عن الاحتجاج او العمل بحديث من الأحاديث فاعلم أنه قد انتقل فى تلك اللحظة الى الزواية الأصولية الفقهية!!
فالمحدث ينتهي من شغله وهو تنقيح الحديث وسبره ونقده وغربلته حتى يعلم حاله من الصحة او الضعف ثم يقدم نتيجة بحثه على طبقة الفقهاء والاصوليين: أنه اليكم الحديث فهو صحيح عندنا او يقول اليكم الحديث فهو ضعيف فى صناعتنا ثم ينصرف، فينظر الأصولي الى الحديث من حيث دلالات الفاظه ليعلم مقتضاه من الوجوب والندب والكراهة والتحريم ثم يستقرأ أدلة الشرع ليتحقق من وجود المعارض فإن وجد فيشتغل بتطبيق قواعد التعارض والترجيح وهكذا.... الخ حتى ينتهي الى أن الحديث صالح لأن يعمَل به. وهذا ينطبق على الحديث سواء كان ضعيفا او صحيحا فالضعيف معمول به في الاحكام وفضائل الاعمال ما لم يكن شديد الضعف او واهيا او موضوعا باتفاق المحققين من المحدثين والفقهاء والأصوليين بشروطه المذكورة فى محلِّه وهو واقع اجتهاد الأيمة الأربعة وغيرهم وليس هذا محل بسط ذلك...
فمن ثم تجد حديثا صحيحا فى البخاري كحديث (انما الماء من الماء) ولم يعمل به عامة الفقهاء مع صحته لكن له معارض... وتجد حديثا ضعيفا فى الترمذي مثلا كحديث (هو الطهور ماؤه الحل ميته) وعليه العمل.... فلذلك تعجبني عبقرية الامام الترمذي فى تسميته لسننه «الجامع المختصر من السنن ومعرفة الصحيح والمعلول وما عليه العمل» فجمع فيه بين صناعتَىْ الحديث والفقه فلذا ذهب الحافظ عبد الله الصديق الغماري الى تقديم عناية الطالب بسنن الترمذي على الصحيحين لأنه سيتدرب على الصناعتين معا:
وعدد أحاديث سنن الترمذي (٣٩٥٦) فيها الصحيح والحسن والضعيف ومع ذلك يقول الترمذي فى العلل {جميع ما فى هذا الكتاب من الحديث - أي أحاديث الأحكام صحيحا وحسنا وضعيفا - معمول به وقد أخذ به بعض أهل العلم ما خلا حديثين} فذكرهما مع أنه نازعه فى الحديثين ابن رجب الحنبلي فى «شرح العلل» والحافظ احمد الغماري فى «المَثْنَونِي والبَتَّار» أن الحديثَين أيضا معمول بهما.. نعم! ليس فى هذا تعطيل وتضيق نطاق علم الحديث فهو فيحاء واسع كما ان المحدث يكون فقيها اصوليا فى نفس الوقت وهو المطلوب اذ ذلك سبب تأليف الخطيب البغدادي كتاب «الفقيه والمتفقه» بل هو الداعي الى تأليف الرامهرمزي كتاب «المحدث الفاصل بين الراوي والواعي»وهذا كان الأصل قبل تصنيف الفنون وتمييز بعضها عن بعض. فمن جمع بينهما فقد تحقَّق.
إبراهيم نياس شرو
Click here to claim your Sponsored Listing.