Babu al'ummar da za ta ci gaba sai da shugaba ko shugabanci na gari. Shin ta yaya za mu gane alamomin shugaba na gari ko kuwa wanda za mu yi zaton shugabanci na gari daga gareshi. Wannan yana da muhimmanci kwarai musamman a halin yanzu da yan siyasa ke anfani da hanyoyi daban-daban don cinma burinsu, amma kwalliya bata biyar kudin sabulu ga yan kasa.
Ga kadan daga cikin siffofin shugaba na gari:
Kamala da kyau manufa
Duk shugaba in dai nagari ne yana da kamun kai, wato yakan kasance mai nisantar da kai daga wasu dabi’u dake durkushe kima cikin al’umma, misali, yawan shaye-shaye, da neme-nemen mata, da fadace-fadace ko zage-zage. Haka kuma shi shugaba na gari yana da manufa mai kyau akan al’uma. Za a fahinci hakan ne ta hanyar dubi ga yanayin rayuwarsa a cikin mutane da karfin tausayi da yake da shi.
Hukunci da hukuntarwa
Shugaba na gari zai gina tsarin mulkinsa akan dokokin kasa da tabbatar da hukunta duk wanda ya take doka. Da farko dai, shi zai zamo mai bin dokan. Yin haka shi zai ci da kasa gaba maimakon kowa ya zama mai daukan doka a hannunsa.
Za a iya karanta: Sirrantattun matsaloli dake kawo cikas a shimfidar aure
Natsuwa da Hangen nesa
Duk lokacin da aka wayi gari shugaba bai da natsuwa, babu ko shakka mulkinsa zai kare abirkice. Komi na bukatar tunani don dora komi akan muhalli da ya dace. Hakan na nuni da cewa shugaba na da baiwa na hangen nesa yanda zai ci da al’ummarsa gaba.
Rashin tsatsauran ra’ayi
Tsasauran ra’ayi a nan na nufin yanke hukunci dake da alaka da tunaninsa shi kadai. Irin wannan ra’ayi shike haifar da mulkin k**a karya, mulki da talaka bai da ‘yancin baiyana kukansa.
Girmama karfin mulki
Mu sani cewa duk shugaban da yake girmama matsayin sauran ma’aikata dake aiki a karkashinsa, shugaba ne nagari. Hakan na nufin zai iya baiwa kowa hakkin aikinsa da daraja daidai da yanda karfin doka ta ba shi.
Halaye da za mu gane shugaban kwarai suna da yawa. Wannan dan kadan na kawo daidai gwargwadon fahimtata. Allah ya albarkacemu da shugaba
Shugaba Ñagari muke fata
We have open this page to continue awareness ,educating, entrainment, about today life
Vous voulez que votre école soit école la plus cotée à Kinshasa ?
Cliquez ici pour réclamer votre Listage Commercial.
Cliquez ici pour réclamer votre Listage Commercial.
Emplacement
Contacter l'école
Téléphone
Site Web
Adresse
Kinshasa