09/09/2022
ALLAH YA TSARE MANA IMANINMU
Shin Da Gaske Ne Sarauniya Queen Elizabeth Ta Haɗa Nasaba Da Manzon Allah (SAW).?
Bayan Tozali Da Ababen Da Ake Ta Yadawa, Dan Gane Da Ikirarin Sarauniya Elizabeth Na Kasancewar Ta Jika Ta Allah (SAW) A Social Media, Hakan Ne Yabani Damar Bibiyar Diddigi Na Tarihi Domin Tabbatar Dashi.
GA YADDA TARIHIN YA FARO.
Masarautar Banu Umayya Masarautace Ta Larabawa, Wacce Aka Kafata Bayan Wafatin Manzon Allah (SAW), Ta Kasance Da Runduna Mai Karfi, Kuma Tana Da Yanki Mai Tsawo Da Fadi Na Murabba'in Kilometer Million 15, Daga Yankin Kauskasus Wanda Akafi Sani Da (Europe) Zuwa Yankin Iberia Wacce Itace Yankin Musulmin (Spain, Portugal, Adorra, Da Gibraltar) , Daular Banu Umayya Itace Ta Biyar Cikin Mafiya Karfin Masarautun Duniya, Wacce Take Mulkar Mutane Akalla Million 62, Cikin Adadin Mutanen Duniya A Wannan Lokaci.
Babban Birnin Mulki Na Daular Banu Umayya Itace "Kardoba" Wanda Ayanzu Ita Ake Kira Spain, Wacce Ta Kasance A Tsakanin Shekarar 758 Da 929.
Birnin "Kardoba" Ta Zamo Cibiyar Al'adu Da Harkokin Karatu Da Addini, Ga Al'ummar Musulmai, Kristochi, Da Kuma Yahudawa, Inda S**a Kasance Sun Bunqasa A Fannin Ilmin Kimiyya, Tarihi, Ilmin Kasa (Geography) Da Ilmin Falaki, Da Kuma Lissafi,
Sannan Kuma Ba Abu Bane Mai Sauki Ba, Yiwuwar Auratayya Tsakanin Mabiya Addini Mabambanta, Kamar Musulmi Da Kiristochi, Da Kuma Yahudawa A Wannan Karni.
Faduwar Daular Banu Umayya Yazo Bayan Juyin Mulkin Da Abu Yazid Yayi A Shekarar (661-750 CE) Wanda Shine Na Biyu, Daga Cikin Khalifofi, Na Farko Farkon Tarihin Musulunci.
Daular Abbasiyya, Tsatson Ta Yasamo Ne Daga Abu Al-qasim Muhammad Ibn Abbad, Wanda Malaman Tarihi S**ai Ikirarin Yana Da Dangantaka Ta Jini Kai Tsaye Zuwa Ga Manzon Allah (SAW) Ta Hanyar Diyar Sa Sayyida Fadima (As).
Ta Nasabar Jinin Al Qasim, Malaman Tarihi S**ayi Amannar Cewa "Sarauniya Elizabeth Ta Hada Zuriya Dashi (Sayyadina Rasulullah SAW)
Wannan Shine Cikekken Bishiyar Zuriyar Sarauniya Elizabeth Da Ya Hadata Da Manzon Allah (SAW).
Elizabeth Ta II Sarauniyar Ingila, 'Yar George Na VI, Sarkin Ingila, Dan Gidan George Na V, Sarkin Masarautar Ingila, Dan Edward Na VII Sarkin Ingila, Dan Victoria, Sarauniyar Ingila, Diyar Edward Duke Na Kent Da Strathearn, Dan Geoerge Na III, Sarkin Babbar Burtaniya, Dan Fedrick, Yariman Wales, Dan George Na II, Sarkin Burtaniya, Dan George Na I, Sarkin Burtaniya, Dan Sophia, Zabebbiyar Hanover, Diyar Elizabeth Na Bohemia, Diyar James Na I/V, Sarkin Ingila, Ireland Da Scotland, Dan Mary, Sarauniyar Scotland, Diyar James Na V, Sarkin Scots, Dan Marget Tudor, Diyar Elizabeth Ta York, Diyar Edward Na IV, Sarkin Inglila, Dan Richard Platagenet, Duke Na York, Dan Richard Na Conisburg, Earl Na Cambridge, Dan Isabella, Parez Na Castille, Diyar Maria Juana De Padilla. Diyar Mariya Parnendez, De Henesterosa, Diyar Aldonza Ramires De Confetes, Diyar Aldonza Gonsalez, Giron, Diyar Sancha Rodriguez, De Lara Diyar Rodrigo Rodriguez, de lara, Dan Sancha Alfonsez, Infanta Na Castile Diyar Zaida (Aka Isabella) Diyar Al Al Mu'utamid Ibn Abbad Sarkin Seville (Salibiyun), Dan Abbad Na II, Al Mu'tadi, Sarkin Saville Dan Abu-Al Qassim, Muhammad Ibn Abbad Na II, Sarkin Sevielle, Dan Isma'il Ibn Qara'is Dan Qara'is Ibn Abbad Ibn Amr, Dan Amr Ibn Aslan, Amr Dan Amr Ibn Itlaf, Dan Itlaf Ibn Na'im Dan Na'im Na II, Al Lakhmi, Dan Na'im Al Lakhmi, Dan Zahra Bin Husain, Dan Hassan Ibni Ali, Dan Sayyida Fatima, Diyar MANZON ALLAH (SAW).
YADDA ZURIYAR TA HADU DA MANZON ALLAH (SAW)
Al-qasim Yazamo Shugaban Seville (Salibiyun) A Babban Birnin Musulunci Na Spain, Sannan Yayi Mulki Har Zuwa Mutuwar Sa, A Shekarar 1024 Bayan Halifofi Guda Biyu, Jikan Sa Muhammad Al Mutamid, Yaci Gaba Da Jan Ragamar Mulki A Shekara Ta 1071, Shine Kuma Na Uku Kuma Na Karshe A Sarakunan Daular Abbasiyya
A Shekara Ta 1091, Daular Abbasiyya Ta Fada Hannun Zuriyar Almoravid, Wanda Asalin Sa, Zuriyar Morocco Ne Su Kuma Wata Kabilace Yan Asalin Yankin Arewancin Africa,.
Al-Qassim Yana Da 'Ya Mai Suna Zaida, Wanda Ta Kasance Musulmace Yar Gudun Hijira, Ta Gangara Zuwa Ga Sarki Al-Fonso VI's Court, Sarkin Leon, Castilla, Da Kuma Galicia A Spain.
A Lokacin Da Sarki Almoravids Ya Kai Hari Ga Daular Abbasiyya, Zaida Ta Koma Addinin Roman Katolika, Kuma Ta Auri Sarki Alfanso Na VI, Sai Ta Chanja Suna Zuwa Isabella, Bayan Riddanta. Tare Da Wannan Sarki Sun Haifi Yaya Guda Uku, Wanda Suma S**a Tafi Wajen Samar Musu Wasu Zuriyyar,
Bayan Ficewar Karni Biyu, A Cikin Shekara Ta 1352, Daya Daga Cikin Zuriyar Zaida, Da Sarki Alfonso, Mai Suna Maria De Pedilla S**a Haifi Yaro Da Sarki Peter Na Castille, Wannan Sarki Ya Haifi Yara Hudu Da Ita. Biyu daga Cikin Su Sai S**a Auri 'Ya'yan Sarki Edward Na III, Na England. Daga Cikin Wannan Zuriyar Tasu Sarauniya Elizabeth Itama Aka Haifeta, Ta Samu Kalarta, Da Kuma Sarautarta, Daga Dukkanin Zuriyar Mutanen Yammaci Da Kuma Mutanen Gabashi.
DAGA Shafin Dokin Karfe TV