Darul-Sufiyyah

Darul-Sufiyyah

Share

A Service of awareness to Tijjaniyah fiollowers

11/07/2024

Muna Bukatar Members suyi Mana Magana Musamman daga Garuruwan Jihar katsina

Photos from Darul-Sufiyyah's post 16/04/2024

AI MANA ADALCI MANA

1. Mutane suntashi tunda Asuba, sunyi Sallan Asuba cikin Jam'i sunzauna sun karanta:

Fatiha x1
Istigfari x100
Lã ilaha illallahu x100
Salatul Fatih x100

Kace sunyi aikin banza tunda ba Shugaba ﷺ yasasu ba.

2- Bayan Sallan Lã'asar sunsake zaunawa s**a karanta:

Fatiha x1
Istigfari x100
Lã ilaha illallahu x100
Salatul Fatih x100

Shima kace sunyi aikin banza.

3- Sunsake zaunawa tsakanin Sallan Magriba da Isha'i sun karanta:

Fatiha x1
Istigfari x30
Lã ilaha illallahu x100
Salatul Fatih x50
Jauharatul Kamal x12

Bayan sungama s**a karanta
Hasbunallahu x450
Yã Laɗifu x129

Sannan s**ayi Adu'an Allah yajikan iyaye da Malamai (wanda aciki harda naka iyayen) yakuma zaunarda ƙasan mu Najeriya lafiya.

Shima kace sunyi aikin banza tunda Annabi ﷺ beyi ba kuma baice suyi ba.

4- Akowata Ranan Juma'a bayan ƙarfe 5:30pm sunka zauna suyita karanta Lã ilaha illallahu harzuwa lokacin Sallan Magriba. Haka zalika shimadai kace sunyi aikin banza tunda Annabi ﷺ beyi ba kuma baice suyi ba.

5- Sunje taron Mauludi inda acan ma sunyi karatun Al-Qurani, sunyi ma Annabi ﷺ Salati, sunkaranta hadisai sannan kuma s**a karanta tarihin shi.

Ananma dai kace sunyi aikin banza tunda Annabi ﷺ beyiba kuma bece suzauna suyi ba.

6- Ɗan Uwansu Almajiri yayi sabon gida yatarasu a gidan s**ayi mashi saukan Al-Qurani domin neman albarkan Ubangiji da kariya daga sharrin shaiɗanu shima kace sunyi aikin banza.

Kaikuma yau gashi kanayin abubuwa dayawa da Shugaba ﷺ beyiba kuma bece ayiba kuma sunfito sunyi maka irin tambayoyinda kake masu kuma ka kasa bada irin amsarda kakeson subaka.

Saboda haka s**ace kaima Bidi'a kakeyi duk kabi kanatajin haushinsu😂😂 Bayan kuma kai kace duk abunda Shugaba ﷺ beyi ba, baice ayiba koda kayishi kayi Bidi'a. Ita kuma Bidi'a ɓatace kuma dukkan mai aikata Bidi'a Ɗan wuta ne.

YA ALLAH KA ƘARA SHIRYAR DA MU ALFARMAR SAYYIDINA MUHAMMAD SAW🤲

09/04/2024

GAGGAWA AKE, MUTUWAR SHEHU?

~Duk Ranar da Maulanmu shehu dahiru Usman bauchi RTA yayi wafati
:
______ ko ba'a fadawa kowa ba wallahi sai kowa yaji ajikinsa.
:
Saboda haka kuyi hakuri ku Daina gaggawa domin wallahi bazaku san cewa irin su maulan mu shehu dahiru Usman bauchi RTA Wata garkuwa bane ba garemu Yan Nigeria da ma Africa Baki daya ba sai Ranar da yayi wafati,

Ya Allah ka karawa maulan mu shehu dahiru Usman bauchi RTA lafiya da Nisan kwana albarkarcin annabi sallalllahu alaihi wasallam 🤲🤲🤲

Amma kucigaba su Sheikh Abul fathi sani Attijjani ne gasu Nan daidai daku wallahi zasu ci uwar kowa da hujjah har inda ba,a xungurowa kunsanshi zai rushe shi shi ba damuwarsa ba ne

Photos from Darul-Sufiyyah's post 21/03/2024

TARON MUSULMI NA DUNIYA

Maulana Sheikh professor Ibrahim Ahmad Maqari ya gabatar da Lecture a taron malaman duniya da ya gabata a kasar Saudi Arabia da kasar Morocco.
An yi taro lafiya an kare lafiya.

17/03/2024

Wato saudiyya ta gano sufaye sune cikakkun Ahlussunnah,yanzu haka prof.Maqari Yana can ya gabatar da lecture a Rabidatul Alami 🙏

28/02/2024

TARIHIN SHEIKH MUSTAPHA MAGAJI ALIYU MALUMFASHI...

Sunansa : Mustapha Magaji Aliyu.
Sunan Mahaifinasa : Aliyu.
Sunan Mahaifiyarsa : Suhaiba.
Sunan Kakansa: Alkali Abubakar.
Alkali Abubakar Jikane gun Shehu Usman Danfodio.

Alkali Abubakar shine Limamin Farko kuma Alkalin Farko agarin Malumfashi.

Anhaifi Shehu Mustapha Magaji Aliyu Malumfashi a shekarar 1954.

Karatunsa:
1. Galadima Model Primary School Malumfashi
1962.
2. ATC Katsina 1977-1981.
3. ABU Zaria 1987-1988.
4. Police College Kaduna 1973.
5. Military School Zaria.

Aikin da yayi:
1. Malamin Makaranta 1976- 1977.
2. Alkali 2002-2016.

Malamansa agarin Malumfashi:-
*Yafara karatu gun Mahaifinsa.
*Sheikh Yusuf Ahamad Maijalalaini (Alqur'an)
*Malam Moh'd Maijaki.
*Malam Lawal Magini.
*Malam Abubakar Bube Gangarawa.
*Malam Moh'd Idris Kwaine Gangarawa.
*Malam Salihu Gangarawa.
*Malam Haruna Na Limamin.
*Malam Shehu Gwamutsawa.
*Malam Hamisu Danfili.

Malamansa a Katsina:
*Malam Moh'd Salihu.
*Malam Dahiru Unguwar Alkali Katsina.
*Malam Suhaiba Safana.

Gudunmawarsa ga Addinin Musulunchi.
"Ya kafa Makarantar Islamiyya a Malumfashi 1982.
"Yafara Wa'azi a Jahar Katsina 1978 karkashin Darikar Tijjaniyya.
"Makarantar Labarabchi a:
1. Gangara Kaduna.
2. Giwa Kaduna.
3. Marabar Maska Funtua.
4. Director Maijalalaini 2001-2020.

Ya amshi Darika gun Shehu Jafaru Katsina a 1977.

Yayi Tarbiyyarsa a gun Shehu Ahmadu Tingilin.

Mukaddamanchi:
1. Sheikh Idris Mai Malali Kano.
2. Sheikh Aliyu Harazimi Kano.
3. Sheikh Abulfatahi Maiduguri.
4. Sheikh Umar Asuffy Assingali.

Tafiye tafiyensa Dan Yada Addinin musulunci.

Yashiga Lungu da sako na Jihar Katsina, Kaduna,Kano, Niger da sauran sassan Nijeriya don yada addini musulunci.

Shehu Mutum ne Mai ban Dariya, iya bada Misali da iya Isar da Sakon Allah.

Ya Mutu Yabar Mata biyu da Yaya.

Allah Yajaddada Rahama garesa Amen.

Abdulfatah Shehu Makarfi...

Photos from Darul-Sufiyyah's post 12/02/2024

Tinubu ya gana da shugabannin Tijjaniya na duniya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce akwai buƙatar haɗin kai tsakanin Shugabannin addini da na siyasa wajen ciyar da ƙasa gaba.

Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da yake karɓar baƙuncin shugabannin Ɗariƙar Tijjaniya na duniya wanda Khalifa Muhammad Mahe Niass, ya jagoranta.

Tinubu ya ce gwamnatinsa a shirye take wajen ciyar da harkokin addini ga wadanda suke taimakawa wajen gida ƙasa.

Ya ce burinsa " mayar da Najeriya ƙasar da za ta iya ciyar da kanta ta hanyar noma, har ma ta samu rarar da za ta iya fitar da ita kasashen ketare.

Da yake nasa jawabin a madadin wakilcin masu ziyarar Khalifa Muhammad Mahe Niass ya yaba wa Gwamnatin Tinubu yajen ƙoƙarin da take yi na ganin an samu zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya.

Yayin ziyarar tawagar ta yi addu'ar samun zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya da nahiyar Afrika da duniya baki ɗaya.

11/02/2024

Wai yanzu wadannan ake kira YAN BIDI'A, Kuma wanda aka tara wadannan Mutanen dan shi SHEHU IBRAHIM NYASS wasu ke wulakantawa?

Photos from Darul-Sufiyyah's post 11/02/2024

MATAIMAKIN SHUGABAN KASA KASHIM SHETIMA NE YA WAKILCI SHUGABA BOLA TINUBU WAJEN MAULIDIN KASA NA SHEHU DA AKA GABATAR A ABUJA.
Allah ya sa kowa ya koma gida lafiya?

Photos from Darul-Sufiyyah's post 10/02/2024

YAU AKA GABATAR DA TARON MAULIDIN SHEIKH IBRAHIM NYASS A ABUJA. Ko wane fatan Alkhairi gareku?

10/02/2024

ALLAH KE NAN: Wanda ya ce baya son taimakon Annabi SAW ko ya ake ciki yanzu ga yan sanda na neman shi ruwa a Jallo?

05/02/2024

AN SAKE KAI WANI HARIN KUMA A KATSINA

Yayinda da ake cikin jimamin harin Sabuwa inda yan ta'addar daji sunka tafi da yan biki har su 52, an sake kai wani harin a karamar hukumar kankara

Harin dai ya faru da Yammacin ranar Lahadi tsakanin Magariba zuwa Isha'i 'lokacin da Yanbindiga s**a kai hari a wani gari Katsalle a kusa da garin Mabai dake da nisan kilomita sha biyar (15) zuwa karamar hukumar Ƙanƙara ta jihar Katsina inda s**a Kashe wani mutum mai suna Mustafa, da jikkata wani Rabi'u tare da ƙona gidansa gaba ɗaya.

Haka kuma yan ta'addar masu garkuwa da mutane sun kwashi mata da ƙananan Yara da ya kamar yadda rahotanni ke nuna ba a iya Tantance su ba.

"Muna cikin tashin hankali bamu da wani sukuni muna ta addu'o,i a ko ina a masallatai, muna kuma neman dauki daga jami'an tsaro da Gwamnatin jihar Katsina, ɓarayin nan ƙara shigo mana kawai suke har a garin Mabai" cewar Aqibu Abdullahi mazaunin garin da aka zanta da shi.

Duk da nasarorin da jami'an tsaron ke samu a wasu yankunan. Hare-haren 'yanbindigar a wasu yankunan na jihar Katsina yana kara ta'azzara ko a cikin satin da ya gabata ankai makamancin irin sa a Tashar Bawa dake kan iyakar Kaduna a karamar hukumar Sabuwa wanda yanbindigar s**a kwashe fiye da mutum hamsin s**ai garkuwa dasu.

Want your school to be the top-listed School/college in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Katsina